Ana cece-kuce bayan ganin alƙalin da ya yi hukuncin rikicin siyasar Ribas da Wike a biki

Daga BELLO A. BABAJI

Cece-kuce ya ɓarke a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta, sakamakon ganin Ministan Abuja, Nyesom Wike tare da Alƙali, Emmanuel Agim, wanda shi ne na Kotun Ƙoli da ya yi hukuncin rikicin siyasar Jihar Ribas, a wani taron bikin yaye ɗaliban Jami’ar Kalaba (UNICAL) dake Jihar Kuros-Riba.

A ranar Asabar ne aka gudanar da taron karo na 37 a shekaru 50 da samar da jami’ar.

Hotunan da aka wallafa a Soshiyal Mediya sun nuna Wike zaune a layin gaba tare da Agim da kuma Ekaetta Akpabio, wadda ita ce matar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Hukuncin rikicin siyasar Ribas da aka yi a ranar 28 ga watan Fabrairu ya taimaka wajen sanya dokar ta-ɓaci a jihar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ƴan kwanakin nan.

A yayin bikin ne aka karrama Wike da matsayin dakta a ɓangaren harkar Shari’a.

Ana ganin akwai lauje cikin naɗi duba da cewa Alƙali Agim shi ne wanda ya yi hukunci game da rikicin siyasa a Ribas, lamarin da ya sa wasu ke ganin harkar demokraɗiyya a Nijeriya ta lalace yayin da wasu ke alaƙanta hakan da lalacewar harkar shari’a a Nijeriya.

Saidai, a wata takarda da Jami’in Hulɗa da Jama’a kuma Daraktan Labarai na Kotun Ƙoli, Dakta Festus Akande ya fitar, ya ce Mai Shari’a Agim ya halarci taron ne kasancewar ya na ɗaya daga cikin waɗanda aka gayyata, ba wai rakiye ga wani ɗan siyasa ba.

Ya ce, batun da ke yawo na cewa ya raka Wike ne zuwa bikin, batu ne na ƙarya wanda babu ƙamshin gaskiya acikin sa, ya na mai cewa Agim ɗaya ne daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar don haka ne aka gayyace shi kuma aka karrama shi da matsayin dakta.

Ya kuma yi kira ga al’umma da gidajen jaridu da su riƙa tantance labari gabannin yaɗa shi don kauce wa haifar da ruɗani acikin al’umma.