Ana gallaza wa ɗalibai Musulmai a jami’o’i mallakin Kiristoci a Nijeriya – MURIC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Kare Muradun Musulmai a Nijeriya (MURIC) ta yi zargin ana gallaza wa ɗalibai Musulman da ke karatu a jami’o’i musu zaman kansu mallakin Kiristoci a ƙasar nan.

Ƙungiyar ta faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa wacce Shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya sa wa hannu, ta kuma fitar a ranar Alhamis.

A cikin sanarwar, MURIC ta zargi jami’o’in da nuna gaba da tsana da kuma tsangwama ga Musulmi da kuma adddinin Musulunci ta hanyar yadda ake tirsasa ɗalibai Musulmai zuwa Coci da kuma hana su sa hijabi da sauransu.

“Mun samu rahotanni da yawa kan yadda jami’oin masu zaman kansu mallakin Kiristoci ke nuna wa ɗalibai Musulmai kyama da kuma wariya, ta yadda ba sa iya yin addininsu yadda ya kamata.

“Sannan kuma ba a barin su su kafa tare da gudanar da ƙungiyarsu ta ɗalibai mai alaƙa da addinin Musulunci, mafi muni ga wannan shi ne rashin ba su inda za su yi ibadarsu.

“Haka kuma ana tilasta musu zuwa Coci yin ibada, a inda ake ɗaukar sunaye, waɗanda duk ba su halarta ba, kuma a hukunta su,” a cewar MURIC a cikin sanarwar.

Shugaban na MURIC ya ce hakan take haƙƙin ɗalibai Musulmi ne da Kundin Tsarin Mulkin ƙasar nan ya ba su, ya kuma yi kira ga hukumar kula da jami’oi ta ƙasa da ta gaggauta tsaftace waɗannan jami’o’in.