Ana jigilar manyan ƙarafun gadar Cocody daga Sin zuwa Kwadibuwa

Daga CMG HAUSA

Jiya Asabar 16 ga wata, jirgin ruwa dakon kaya na farko ya kwashi manya ƙarafuna guda 37 waɗanda za a yi amfani da su domin aikin gina gadar Cocody ta ƙasar Kwadibuwa, gadar mai madaurai mafi girma a yankin yammacin Afirka, ya tashi daga tashar ruwan kogin Yangtse dake birnin Nantong na lardin Jiangsu na kasar Sin, zuwa ƙasar ta Kwadibuwa.

Gadar Cocody mai tsawon mita 630, muhimmin aiki ne na haɗin gwiwa a tsakanin kasar Sin da ƙasashen Afirka, idan aikin ya kammala, wanda kamfanin ƙasar Sin ke gudanarwa, za ta kasance gada mai madaurai mafi girma a yankin yammacin Afirka.

Mai fassarawa: Jamila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *