Ana sa ran yi wa mutum miliyan ɗaya gwajin hawan jini da ciwon suga a Jihar Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ƙoƙarin da aka fara na gangamin kawar da cutar hawan jini da ciwon suga, da ake sa ran yi wa mutane miliyan 10 a faɗin ƙasa, an buƙaci al’ummar Jihar Kano da su fito domin yi musu gwajin na hawan jini da ciwon suga.

Kwamishinan lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan kira, yayin fara aiwatar da shirin a harabar hukumar samar da magunguna da kayayyaki ta jiha (DMCSA).

Shirin gangamin mutane miliyan 10 ya mayar da hankali ne ga cututtuka marasa yaɗuwa, musamman hawan jini da ciwon suga, waɗanda ke taka rawa wajen haifar da cututtuka da mace-mace a Nijeriya, da ya sanya zauren Kwamishinonin lafiya na Nijeriya ya himmatu wajen magance matsalar, wanda gangami ne na ƙasa baki ɗaya da ke da ƙudirin yi wa ‘yan Nijeriya miliyan 10 gwajin hawan jini da ciwon suga a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya na Abuja, a tsawon mako guda.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya aikewa Manhaja ranar laraba, ya ce, daga cikin manufofin shirin akwai yi wa al’ummar Nijeriya miliyan 10 gwajin hawan jini da ciwon suga da haɗa sakamakon da aka tabbatar da hanyoyin samun waraka, da samar da magunguna na ƙaramin zango daidai da tsarin da ya dace, da ƙara wayar da kan al’umma da ilimantar da su game da hawan jini da ciwon suga, da ilimantar da al’umma game da abincin da za su rinƙa ci, da motsa jiki, da kaucewa shan taba, da sauransu.

Dakta Labaran ya buƙaci mutane da su shigo a dama da su a cikin wannan aiki don tabbatar da yadda matakin lafiyarsu yake, ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da waɗannan cututtuka za a ba su magani kyauta ko kuma a tura su asibiti mafi kusa domin a ci gaba da kula da lafiyarsu idan an fahimci larurar tasu babba ce.

Kwamishinan ya shawarci jama’a da su kai iyalansu wuraren da aka ware don yin gwajin a cibiyoyin da aka tanada don yin aikin kyauta har tsawon mako guda a faɗin jihar Kano, yana mai fatan yi wa mutane miliyan ɗaya a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Ya ce “Aikin wanda zai lashe kusan Naira miliyan 800, babba ne. Saboda haka, mutane, daga kan ɗan shekara 20 zuwa sama, kawai buƙatar su yi cikakken amfani da wannan dama wajen yin gwajin waɗannan cututtuka masu hallakarwa. Waɗanda aka samu da ɗaya ko kuma duka daga cikin cututtukan kada su razana, maimakon haka su gode wa Allah saboda an gano wata cuta da ta ɓuya a jikinsu, domin su nemi waraka.

Dakta Labaran ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake nuna damuwa da lafiyar al’ummar Jihar Kano a kowane lokaci, ya kuma jinjina wa ƙungiyoyi masu tallafa wa fannin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suke bayar da gudummawa wajen ci gaban lafiya.