Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yar majalisar dattawan Nijeriyar nan da majalisar ta dakatar bisa zargin nuna rashin ɗa’a ga zauren, Sanata Natasha Akpoti ta ce majalisar ta koma tamkar ta ‘yan kungiyar asiri.
Sanata Natasha wadda ta bayyana hakan a wata tatttaunawa da kafar BBC, ta ƙara da cewa ta yi “imanin cewa mutane na tsoron tofa albarkacin bakinsu a zauren.”
“Akwai irin al’adar nan ta tsoro a tsakanin ‘yan majalisar. Idan ka kuskura ka soki shugaban majalisa ko ka bayyana saɓanin ra’ayi to fa kun yi kasadar a toshe maka duk wata dama kuma ba za ka samu damar yin magana ba,” inji Sanata Natasha.
Dangane kuma da zargin lalata da ta yi wa Sanata Godswill Akpabio, Natasha ta ce tana da hujjoji kamar haka:
“Abin ya fara ne a shekarar 2023 a ranar 8 ga watan Disamba inda muke gidansa da ke shiyyar da ya fito inda ya zagaya da mu gidan nasa tare da mijina. Yana riƙe da hannuna yayin da mijina yake tafe a bayanmu. Sai muka shiga wani ɗaki kuma bayan da ya lura akwai tazara tsakaninmu da mijin nawa sai ya latsa min tsakiyar hannuna abin da mu mata mun san abin da hakan yake nufi na sha’awa idan namiji ya latsa miki hannunki.
“Sai ya ce yanzu kina majalisar dattawa zan ƙirƙiri lokaci da za mu zo nan mu ji daɗi. Amma da yake muna cikin wani yanayi na kamala ban yi yunƙurin tayar da wani rikici ba saboda abokantakar da ke tsakaninmu ta gaske. Mijina yana girmama shi sosai.”
“Akwai wani lokaci da ina sauri zuwa majalisar sai na manta ban saka zobena ba. A wajen akwai wasu sanatoci kusan guda biyar sai suka ce Natasha yaya haka ba ki sanya zobenki ba ko dai wata hanyar ce ta cin amanar maigidanki? Akwai kuma wani lokacin da ya faɗa min cewa Natasha mijinki yana jin daɗinki da alama za ki iya jujjuya da lanƙwasa ƙugun nan naki mai kyau.. Shi ya faɗi haka, su kuma sauran suka kwashe da dariya.”
BBC ta kai ƙorafinta ofishin shugaban majalisar, inda Mataimakin Mai Tsawatarwa Sanata Onyekachi Nwebonyi ya ce:
“Babu wani lokacin da shugaban majalisar…. ya yi yunƙurin yin lalata da Sanata Akpoti a gidansa… ko ya furta kalaman da ba su dace ba a majalisa.”
Ya kuma yi watsi da ƙorafin cewa ana son rufe bakin Sanata Natasha inda ya ce: “Halayen Natasha a majalisa ba su nuna hakan ba.”
Majalisar dattawan Nijeriyar dai ta dakatar da sanata Natasha ne na tsawon wata shida bisa shawarwarin da kwamitin ɗa’a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da sanata Natasha ta miƙa wa majalisar ranar Laraba.
Shugaban kwamatin, Sanata Neda Imasuen shi ne ya bayar da shawarwarin bayan karanto jerin laifuka da kwamitin ya ce ya samu Sanata Natasha da aikatawa a majalisar.
Da yake karanta bayanin dakatarwar, shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio wanda a kansa ne Sanata Natasha ke ƙorafin cin zarafi na lalata, ya nemi jin ra’ayin ‘yan majalisar kan su amince ko su ƙi amincewa da dakatarwar ta tsawon watanni shida amma kuma za a iya rage yawan lokacin idan har ta rubuto takardar neman afuwa. ‘yan majalisar kuma sun amince da hakan.