Ana wata ga wata: NDLEA na neman DCP Abba Kyari wurjanjan bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi

*Kyari ya faɗa a komarmu – ‘Yan Sanda

Daga BASHIR ISAH

Kawo yanzu dai DCP Kyari ya faɗa a komar ‘yan sanda, ‘yan sa’o’i bayan da Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta bada sanarwar tana nemansa ruwa a jallo bisa zargin fataucin muguwar ƙwaya.

Majiyar MANHAJA ta ce an ga lokacin da aka shigo da Kyari babban ofishin ‘yan sanda da ke Abuja da ankwa a hannunsa.

Tun farko dai Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta bada sanarwar tana neman dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan nan, wato DCP Abba Kyari, ruwa a jallo bisa zargin sa da hannu a harƙallar muguwar ƙwayar nan da aka fi sani da hodar ibilis.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da hukumar ta shirya a babban ofishinta da ke Abuja a ranar Litinin.

NDLE tana zargin DCP Kyari kan cewa shi mamba ne na wani kamfanin da ya yi ƙaurin suna a harkar fataucin miyagun ƙwayoyi wanda ke gudanar da harkokinsa tsakanin ƙasar Brazil zuwa Habasha da kuma Nijeriya. Hukumar ta ce Kyari ya ƙi bai wa jami’anta haɗin kai don gudanar da bincike kan lamarin yadda ya kamata ya sa ma ta bada sanarwar tana nemansa ruwa a jallo.

Idan za a iya tunawa, kafin a dakatar da shi daga bakin aiki, Kyari shi ne jami’in da ke kula da rundunar sirri ta musamman na ofishin Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya.

A baya, Cibiyar Bincike ta Ƙasar Amurka ta tuhumi Kyari kan yana da hannu dumu-dumu a maguɗin dukiya wanda ke da alaƙa da gawurtaccen ɗan damfarar nan, Ramon Abbas wanda aka fi sani da suna Hushpuppi.

Sanarwar manema labarai da NDLEA ta fitar a wannan Litinin ɗin ta nuna cewa, “Dole ne ta sanya muka bada sanarwar neman DCP Abba Kyari wurjanja, tsohon kwamandan rundunar IRT.

“Bisa la’akari da bayanan sirrin da muka samu, mun yi amannar cewa DCP Kyari mamba ne a wani kamfanin fataucin miyagun ƙwayoyi, mai gudanar da harkokinsa tsakanin Brazil da Habasha da Nijeriya, don haka muke nemansa don ya amsa mana tambayoyi kan binciken da ke gudana wanda ya zama jigo a cikinsa. Ƙin amincewa da ya yi wajen bada haɗin kai, hakan ya tilasta hukumar shirya taron manema labarai.”

NDLEA ta ce, “Wannan badaƙalar ta soma ne a ranar Juma’a, 21 ga watan Janairun 2022 bayan da DCP Kyari ya kira ɗaya daga cikin jami’an NDLEA ta waya a Abuja, da misalin ƙarfe 2:12 na rana, inda ya faɗa masa cewa zai zo ya same shi bayan an sauko daga Juma’a don su tattauna kan wani batun bincike.

“Ya bayyana a wurin da suka yi za su haɗu da jami’in sannan kai-tsaye ya soma magana a kana bin da ya kawo shi, cewa tawagarsa sun kama wasu masu fataucin miyagun ƙwayoyi da suka shigo ƙasa daga Ethiopia da hodar ibilis mai nauyin 25kg. Sai ya yi masa tayin cewa shi da tawagarsa su ɗauki 15kg na hodar sannan ya bar ragowar 10kg a hannu waɗanda aka kama su da hodar a Inugu. Sannan za a musanya hodar mai nauyin 15kg da ta jabu. Daga nan ya buƙaci jami’in da ya tabbatar da hukumar NDLEA ta Abuja ta bada haɗin kai wajen harƙallar.”

A cewar Femi Babafemi, “Duk wanda ya san haƙiƙanin irin sake ɗamarar da NDLEA ta wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi tun daga ranar 18 ga Janairun 2021 ya san cewa wannan al’amari shuka ce aka yi kan idon makwarwa, saboda jami’anmu sun amince su jajirce a bakin aiki, kuma abin da Kyari ya nema ba mai saɓuwa ba ne a sabuwar hukumar NDLEA.”

Jami’in ya taɓo kwatankwacin wannan badaƙalar wadda ta shafi wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi Ejiofor Felix Enwereaku a Mayun 2021, inda ya shigo Nijeriya daga Brazil don neman a sako masa hodar ibilis ɗinsa mai nauyin 27.95kg da NDLEA ta kama a MMIA. Lamarin da ya kai ga ɗan harƙallar ya bada cin hanci na $24500 amma jami’an NDLEA suka ƙi yarda su bada kai bori ya hau.

“Da misalin ƙarfe 11:05 na safe na ranar Litinin, 24 ga Janairu ne hukumar ta bai wa jami’inta damar yin abin da Kyari ya buƙata, daga nan Kyari ya ci gaba da tuntuɓar jami’in ta manhajar WhatsApp, inda jami’in ya shaida wa Kyari cewa hukumarsu ta amince da buƙatarsa.

“A daidai wannan lokaci kuwa, Kyari ya bayyana cewa an riga an cire kason hodar na 15kg an raba wa jami’an da suka taimaka da bayan sirri kan kama hodar da aka yi da kuma jamia’n rundunarsa na IRT na ‘yan sanda. A cewarsa, kason 7kg aka bai wa ‘yan leƙen asirin sannan aka miƙa wa jami’an tawagarsa kason 8kg an ringaya an sayar da shi.

“Dagan an sai ya yi tayin biyan tawagar NDLEA, (wato jami’in nan da kuma ofishinsu na Abuja) ta hanyar sayar musu da hodar (kason 10kg) a madadinsu, wanda hakan zai sake rage hodar ta asali da ke hannun waɗanda ake tsare da su zuwa 5kg kan Naira miliyan 7 kan kowane giram 1, kuɗin 5kg na hodar ya kama Naira miliyan 35m kenan idan aka kwatanta da canjin Dala a N570 kan farashin kasuwar bayan fage a wannan rana, 24 ga Janairun 2022. A ƙarshe dai zai miƙa wa tawagar NDLEA kuɗi $61,400 kenan.

“Haka dai ya ci gaba da matsa wa jami’inmu lamba kan ya hanzarta ya kammala tsare-tsaren da aka shirya da ofishinsu na Abuja don hodar ta zama a ƙarƙashin kulawarsa. A wannan lokaci kuwa, Kyari na magana ne daga Legas inda ya fake da cewa ya yi tafiya ne don gudanar da wata harkar kansa.

“Washe gari, ranar 25 ga Janairu, Kyari ya buƙaci tura wani ɗan’uwansa don ya miƙa kuɗaɗen sannan jami’ansa su miƙa waɗanda ake zargin amma sai jami’inmu ya ƙi yarda da hakan, maimakon haka sai ya buƙaci su yi harka kai-tsaye tare hannu da hannu, ido na ganin ido amma ba ya wakilta wani ba, don haka ya ce zai jira shi har sai ya dawo daga Legas sannan su haɗu.

“A wannan rana Kyari ya isa Abuja da misalin ƙarfe 5:23 na yamma inda ya haɗu da jami’in a wurin da suka yi haɗuwar farko. Yayin tattaunawarsu, ya bayyana yadda ‘yan tawagarsa suka samu bayanai ta hannun wani ɗan leƙen asiri wanda ya ci amanar masu fataucin hodar, hatta da yadda aka yi jami’ansu suka bar Abuja zuwa Inugu suka kama ‘yan fasa ƙaurin duk ya bayyana masa, da kuma yadda aka ɗebe wani kaso na hodar sannan aka maye da jabun hoda.

“Haka nan, ya bayyana yadda za a iya gane ƙulli biyar na hodar na asali waɗanda za a miƙa wa NDLEA inda ya ce an yi musu alama da jan ɗigo a jikin kowane ƙulli. Dalilin yin hakan kuwa shi ne don gudun kada a ɗauki jabun ƙullin hodar yayin gwaji. Shirin haka shi ne, bayan an tabbatar da cewa lallai 5kg na hodar na asali ne, ka ga ba za a damu da gwajin ragowar ba, wanda kuma su ne na jabun.

“Haka nan ya biyo da kuɗin 5kg a matsayin kason tawagar NDLEA, wanda a jimillanci ya kama $61,400. Sai dai jami’inmu ya ce ya gwammace su je cikin motarsa ya karɓi kuɗin. Saboda an shirya motar ta yadda za ta iya naɗar duk abin da ya gudana a cikinta.”

DCP Abba Kyari

Femi Babafemi ya shaida wa manema labarai cewa, tun ranar Alhamis, 10 ga Fabrairu suka gayyaci DCP Abba Kyari zuwa hukumarsu don ya amsa musu tambayoyi amma har zuwa lokacin da suka tashi aiki ranar Juma’a, 11 ga Fabrairu ba su ga Kyari ba, har ma zuwa lokacin da yake ganawa da manema labarai Kyari bai zo ba.

Ya ci gaba da cewa, ganin Kyarin ya ƙi amsa musu gayyatarsu hakan ya sa NDLEA ba ta da wani zaɓi da ya wuci ta bada sanarwar tana nemansa ruwa a jallo, saboda sai sun ji daga gare shi kafin su gurfanar da waɗanda ake tsare da su gaban kotu.

“Muna sane da irin barazanar kisa da ake yi wa jami’an NDLEA waɗanda aka ɗora a kan wannan bincike, kuma za mu ci gaba da jajircewa wajen bai wa jami’anmu kariya. Masu wannan hali su sani suna ƙara wa kansu matsala ne, walau ta laifin aikata kisa ko cutar da jami’an NDLEA,” in ji Femi Babafemi.