Ana yi wa ƙasashen Afirika turjiya a shirin gasar kofin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An gudanar da wasannin sada zumunta a ranar Talata 27 ga watan Satumba a wani ɓangare na shirye-shiryen gasar kofin duniya na Ƙatar. A ranar 20 ga watan Nuwamba ne za a fara gasar ta ƙasa da ƙasa.

Kamaru ta sha kashi na biyu cikin ƙasa da mako guda, bayan da Koriya ta Kudu ta lallasa Indomitable lions da ci 0-1 a filin wasa na Seoul da ke Koriya ta Kudu.

Bayan wasan Super Sonny da Costa Rica, Koriya ta Kudu sun yi farin cikin kawo ƙarshen wasan sada zumuncin da suka yi da kyau. A ranar Juma’a ne ’yan wasan Uzbekistan suka lallasa Kamaru da ci 2-0.

A Vienna na ƙasar Austria, ranar Talata, Senegal ta riƙe Iran, duk da cewa ’yan wasan Aliou Cisse basu ne suka zura ƙwallon ba, sai dai sun ci moriyar Morteza Pouraliganji na Iran a cikin minti na 55 da fara wasa.

Azmoun ne ya ci wa Iran ƙwallo a minti na 64 da fara wasa, wanda ya baiwa tawagarsa damar kawo ƙarshen wasan da suka tashi 1-1 da Teranga Lions.

Ghana ta ci Nicaragua 1-0, kuma Fatawu Issahaku ne ya zura wa Black Stars a wasan da aka buga na farko a filin wasa na Francisco Artes Carrasco da ke Lorca.

Ita kuwa Tunisia, Brazil ta lallasa ta a Parc des Princes na Faransa da ci 5 da 1.

Morocco ta riƙe Paraguay a filin wasa na Benito Villamarin da ke Seville bayan ta doke Chile da ci 2-0 a ranar Juma’ar da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *