Ana zargin ɗan sanda da yin garkuwa da jariri ɗan sa’o’i 6 a Legas

Daga WAKILINMU

A yayin da ake ci gaba da gudanar da bikin ranar mata na duniya na shekarar 2023, wata Ƙungiyar Kare Haƙƙin Mata ‘Women Advocates Research & Documentation Centre’ (WARDC), ta buqaci a yi adalci kan zargin sace wata jariri ɗan kimanin sa’o’i 6 da haihuwa.

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya da ya gaggauta miƙa ƙarar zuwa hukumar hana safarar mutane ta ƙasa (NAPTIP) a cikin kwanaki 14 ko kuma a kai masa ziyarar zanga-zanga.

Baby Joseph, a cewar wanda ta kafa WARDC, Dakta Abiola Akiyode-Afolabi, wadda ta yi magana a madadin mahaifiyar ’yar, Misis Fortunate Ohafuoso, an ɗauke shi da ƙarfi daga hannun mahaifiyarsa a ranar 23 ga Disamba, 2022, wanda wani ɗan sanda mai suna Mista Samuel Ukpabio, wanda ke aiki a sashin fataucin yara, Panti C.I.D, Yaba da ke Jihar Legas, ya kwace ta daga hannunta.

Da take magana a wani taro da masu ruwa da tsaki da manema labarai a Legas, wanda aka shirya domin tunawa da ranar mata ta duniya ta bana, Akiyode-Afolabi ta ce, “Mun firgita da shiru na tsawon wata guda da Sufeto Janar na ’yan sanda ya yi. Ba za mu iya yin bikin Ranar Mata ta Duniya ba a lokacin da mace ta fuskanci irin wannan mummunan cin zarafi ba tare da samun adalci ba.

“A ranar 6 ga Fabrairu, 2023, an miƙa wata takardar koke ga Sufeto Janar na ’yan sanda don sanar da shi.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da na mata 141 ne suka yi kaca-kaca da Ukpabio bisa laifin yin garkuwa da jariri, Joseph da safarar mutane zuwa hukumar hana fataucin mutane ta ƙasa, NAPTIP, kuma babu wani martani tun daga lokacin.”

“Matar da abin ya shafa ta ruwaito cewa, jami’in ya yi mata barazanar cewa ba za ta tava zuwa ko neman inda jaririnta ya ke ba, yana mai cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin jaririn.

“Wadda abin ya shafa ta ƙara sanar da mu cewa a ranar 24/12/2022, ta kira Mista Ukpabio don neman jaririn ta, kuma jami’in ya sake yi mata barazana ta waya cewa zai kai rahotonta ga hukumar NAPTIP kan zargin safarar yara.

“Ta sake kiransa a ranar 25/12/2022, inda ta ke ƙalubalantarsa da ya haifi jaririn da ta haifa. A nan ne Mista Ukpabio ya buƙaci ta turo da lambar asusun bankinta ya tura mata kuɗi Naira 170,000 (Naira dubu 100 da saba’in) domin ta kula da kanta.

“Wannan matakin da ba a nemi kuɗin ba ya nuna ana zargin an sayar da jaririn. Wadda abin ya shafa dai na cikin dimuwa sakamakon baƙin cikin rasa jaririnta.

Don haka ta roƙi a gaggauta shiga tsakani, inda ta buƙaci da a kama Mista Ukpabio da ƙungiyarsa da ake zarginsa da kuma bayyana inda jaririn da aka haifa ya ke.

Duk ƙoƙarin da manema labarai su ka yi na ganin Mista Ukpabio ya mayar da martani kan zargin, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *