Ana zaton wuta a maƙera..

Daga IBRAHIM YAYA

A kwanakin baya ne, aka buɗe taron ƙasa da ƙasa kan cutar ƙanjamau wato AIDS a birnin Montreal na Canada, taron dake zama irinsa mafi girma kan cutar a duniya, baya kasancewarsa wani muhimmin dandali na yayata matakan kariya da magance cutar.

Galibi masana kimiyya da masu fafutuka daga sassa daban-daban na duniya, su kan yi amfani da wannan dama, wajen tattauna batutuwan da suka shafi yaƙi da cutar ta ƙanjamau.

Sai dai duk da muhimmancin wannan taro, a bana, ɗaruruwan mahalarta daga nahiyar Afrika, ba su samu damar halarta ba kamar yadda aka tsara, saboda wasu manufofi na nuna wariya wajen bada takardun iznin shiga ƙasar ta Canada wato visa da gwamnatin ƙasar Canada ta bullo da su.

Wasu masu ruwa da tsaki kan yaki da cutar kanjamau da suka halarci taro, sun bayyana bacin ransu kan wannan mataki da mai masaukin taron, wato ƙasar Canada ta dauka. Wai ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaka.

A baya ana zargin ƙasashen yamma da nuna wariya da ƙyama da neman bata sunan ƙasashe da ma dakushe ci gabansu, sai ga shi irin wannan mummunan dabi’ar ta ɓulla a ƙasa kamar Canada.

Wannan ne ma ya sa, masu fafutuka ke cewa, bai kamata a riƙa gudanar da irin wannan taro mai muhimmanci dake da nufin kare rayuwar al’umma a ƙasar dake nuna wariyar launin fata ba.

Masu zanga-zanga ma sun bayyana adawa da matakin gwamnatin Canada, na hana daruruwan mahalarta taron shiga ƙasar, galibinsu daga Afrika, saboda rashin daidaiton da ya kai ga ƙaruwar yaduwar cutar. Suna masu bayyana cewa, ya kamata tarukan duniya kan yaki da cutar ƙanjamau, su tabbatar da ana damawa da kwararru daga yankunan da suka fi fama da cutar.

Wani abin takaici shi ne, gwamnatin Canada dai ba ta bayyana dalilanta na hana visar shiga ƙasar ba, amma wasu daga cikin waɗanda ta hanawa visar, sun ce wai ƙasar ba ta yarda cewa, za su koma ƙasashensu bayan an kammala taron ba. Zato dai zunubi, ko da ya kasance gaskiya.

Masu fashin baƙi dai na fatan za a daina amfani da wasu matakai marasa dacewa, wajen mayar da hannun agogo baya, a ƙoƙarin da ake yi na kiyaye lafiyar al’ummar duniya.