APC a Bauchi ta dakatar da shugabanta a matakin gunduma kan yi wa jam’iyya zagon ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi a matakin gunduma ta dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Babayo Aliyu Misau, bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Gundumar Kukadu Gundari a yankin Ƙaramar Hukumar Misau, ce ta dakatar da Babayo Aliyu a matsayin mamba a jam’iyyar bayan da ta zarge shi da aikata wa jam’iyyar zagon ƙasa.

Shugabancin jam’iyyar Gundumar Kukadu ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Zango Lawan da Sakatarensa, Aliyu Hassan Adamu da kuma Mataimakiyar shugabar mata, Asabe Ahmed, shi ne ya bayyana sanarwar dakatarwar ga manema labarai a ranar Asabar.

Sun bayyana cewa sun kira taron gaggawa a ranar Juma’a inda a nan ne suka yanke dakatar da Babayo bayan nazari kan laifukan da ya aikata ciki har da yi wa jam’iyya zagon ƙasa.

Sun ƙara da cewa, ɗaukar wannan mataki ya zamanto babu makawa saboda take dokokin jam’iyya da yake yi.

A cewarsu, an samu Babayo da aikata wa jam’iyya zagon ƙasa kafin da lokacin da kuma bayan zaɓe yayin zaɓukan da suka gudana kwanan baya.

“Muna sanarwa da wannan rana dakatar da Shugaban APC na Jihar Bauchi, Babayo Misau a matsayin mamba na APC.

“Mun ɗauki wannan mataki ne saboda samun shugaban, wanda a yanzu ya zama na dauri, da laifin yi wa jam’iyya zagon ƙasa,” in ji Ibrahim Zango Lawan.

A cewar Sakataren jam’iyyar a gundumar, Aliyu Hassan Adamu, daga cikin laifukan da Babayo ya aikata har da bayyanar da takardar ƙuri’a a lokacin zaɓe wanda ke nuni da jam’iyyar hamayya ya zaɓa

“Abubuwa da dama sun faru wanda ba mu ji daɗin hakan ba…., in ji Sakataren.