APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Boss Mustapha kan zargin ƙin taimaka wa Binani lokacin zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, saboda ya sha ƙasa a hannun Jam’iyyar PDP a lokacin zaɓukan da suka gabata.

Jam’iyyar ta ce Boss Mustapha bai bayar da gudunmawar nasarar da ’yan takarar Shugaban Ƙasa da na Gwamna na APC suka samu a lokacin da ake buƙatar taimakonsa ba.

Da yake sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Yola, babban birnin Jihar, Shugaban gundumar Gwadabawa, Mu’azu Kabiru, ya ce Boss Mustapha bai jajirce wajen samun nasarar APC ba a zavukan.

Ya ce bisa wasu ƙorafe-ƙorafe da ake yi masa, shuwagabannin jam’iyyar ta yanke shawarar dakatar da shi har abada tare da cewa kada ɗaiɗaikun mutane su ɗauki kansu sama da jam’iyyar da ta ba su dama.

Shi ma Sakataren Jam’iyyar APC na Gwadabawa, Abdulkarim Nuhu, ya ce sun yanke wannan hukuncin ne kasancewar yadda Boss Mustapha ke kauce wa a gansa koda an zo wajensa neman taimako ya kuma ƙara da cewa wannan shawarar su da mambobinsu ne baki ɗaya suka yanke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *