APC ba ta san darajar dimukraɗiyya ba – Kwamared Imran Wada

Daga AISHA ASAS a Abuja

Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Cigaban Matasan Arewa (AYDA) kuma ɗan jam’iyyar adawa ta PDP, Kwamared Imran Wada Nas, wanda aka fi sani da shugaban talakawa, ya yi kira ga ‘yan Arewa da su guji zaɓen tumun dare da kuma yin sak a zaɓukan 2023 mai ƙaratowa, inda ya buƙaci da su ajiye jam’iyya, su dubi cancanta don samun shugabanni nagari. 

Wada Nas ya yi wannan jawabin ne a taron manema labarai da ƙungiyar ta kira Alhamis ɗin makon jiya. 

Tun da farko, Nas ya fara da godiya ga Allah da ya ba su ikon yin zaɓen cikin gida lafiya a jam’iyarsu ta PDP, ya kuma jinjina wa jam’iyyar da irin namijin ƙoƙarin da ta yi na ganin an yi zaɓen ba tare da tashin hankali ko cece-kuce ba.

Haka zalika, ya nuna shakku kan yiwuwar zaɓen shugancin jam’iyyar APC, ganin yadda Majalisar Zartarwar Jam’iyyar (NEC) ke ta ɗaga babban taron, da kuma irin rigingimun da ke cikin jam’iyyar mai mulkin ƙasa, ya ce akwai tarin matsaloli a cikin jam’iyyar, waɗanda mutane ba su san da su ba.

Ya ci gaba da nuna cewa jam’iyyar APC tana da ƙishirwar masu tsawatarwa ga waɗanda suka yi ba daidai ba a cikin, saɓanin jam’iyyar su ta PDP da ya ce tana ganin girman na gaba da mutunta muradun kowa da kuma amsan shawarwari. Bugu da ƙari suna da ‘yan kwamitin amintattu (BOT) domin duba ina aka kwana ina kuma aka tashi, tare kuma da neman hanyoyin warware wasu matsaloli da watakila jam’iyyar ke ciki, inji shi.

“Hakan ya sa za ka ga duk abinda ya taso mun warware shi cikin sauƙi. Amma abubuwa da yawa da duk wata cikakkiyar jam’iyya da ya kamata a ce ta mallaka, za ka APC ba ta da su. Wannan rashin abubuwa shi ke sa kowa ya kama gaban shi.”

Wada ya ƙara da cewa hakan ta sa suke ɗaukar Shugaban Ƙasa a matsayin shugaba kuma uban jam’iyya, inda ya yi nuni da Bola Ahmed Tinubu da ake kallo kuma ake kira uban jam’iyyar APC. Ya ce duk inda aka ce akwai shugaban jam’iyya to shi ne uban kowa har shugaban ƙasa, matuƙar shugaban jam’iyya na nan “ya kamata ka tsaya matsayinka na shugaban ƙasa ko gwamna ba shugaban jam’iyya ba,” inji shi.

Ya ce “idan ka tsaya a matsayin ka na shugaban ƙasa ko gwamna, idan shugaban jam’iyya ya zo za ka tashi ka girmama shi kuma ka yi masa abinda duk ya kamata a matsayin shi na shugaba.”

Wada Nas ya ci gaba da cewa irin hakan ta faru tsakanin Sa Ahmad Sardaunan Sakkwato da kuma Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa a matsayin Sardauna shugaban jam’iyya sai kuma Shehu Shagari, wanda dukkan su a cewar sa suna mutunta shugabancin kowa.

Sannan ya kuma nuna rashin gamsuwar sa da masu cewa a yi zaɓen sak a kowace jam’iyya, inda ya ƙara da cewa bai amince da cewar dole sai PDP ta yi takara ko ta ci zaɓe a kowace kujera ba, ya ce kiran shi ga al’ummar Nijeriya musamman ‘yan Arewa su yi cancanta a duk zaɓukan da za a yi a 2023.

“Don haka ni ba na goyon bayan sak, kuma ba na fatan a yi sak, domin duk inda ake yin sak ba ya kawo wa mutane cigaba bare alheri,” ya ce.

Shugaban talakawan ya kwatanta tafiyar dimukraɗiyyar Nijeriya da kwatankwacin nisan Legas zuwa Maiduguri, inda ya ce har yanzu kuma tafiyar ba ta wuce Ibadan ba, kuma har yanzu ba a yi komai ba wajen cigaban dimukraɗiyya a ƙasar. A cewarsa ko lokacin da aka amshi mulkin farar hula a 1999 mutane da yawa lankwashe hannu suka yi suna ganin ba za a yi mulkin dimukraɗiyya saboda saboda katsalandan da sojojin suke wa sha’anin mulkin farar hula.

Wada Nas ya yi kira ga al’umma da masu sha’awar siyasa, mutanen kirki su shigo cikin domin bada tasu gudunmuwar, har yana kwatance da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a matsayin mutumin kirki da ya shigo fagen siyasa a daidai lokacin da Nijeriya ke buƙatar ɗaruruwa irin shi.

“Ina kira ga mutanen kirki su shigo siyasa a dama da su, sai mutane irin su Gwamna Zulum sun shigo cikin siyasa an dama da su sannan tafiyar za ta yi kyau kuma ta yi tsari.

“Mutane su yi haƙuri su kawar ta waɗanda ake ganin ba mutanen kirki ba ne, ba ma su ƙaunar talaka ba ne, su kawo masu ƙaunar su da kuma kishin su. A yi wa marasa mutunci ritaya a siyasa mutanen kirki su shigo,” inji shi.

Ya nuna cewa ya kamata mu yi tunanin makomar ‘ya’yan mu da jikokin mu da ƙannen mu  masu tasowa nan gaba, inda ya ce kada mutane su gaji, kada kuma gwiwowin su su yi sanyi, su fito su zaɓi nagartattun mutane masu kishin ‘yan ƙasa da Nijeriya baki ɗaya.