APC ta ɗage zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta ɗage zaɓen fidda gwani na ’yan takarar shugaban ƙasa zuwa ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni.

An fara gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 29 da 30 ga Mayu.

“Bayan ƙarin wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta yi na gabatar da sunayen ’yan takara daga jam’iyyun siyasa, jam’iyyar APC ta ɗage babban taronta na musamman na shugaban ƙasa daga ranar Lahadi 29 ga wata zuwa Litinin, 30 ga Mayu, 2022 zuwa Litinin, 6 ga Laraba, 8 ga Yuni, 2022,” inji Kakakin jam’iyyar APC, Felix Morka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *