APC ta buƙaci a soke zaɓen gwamnan Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Jam’iyyar APC a Jihar kano ta yi fatali da zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar ɗin da ta gabata, tare da neman hukumar zaɓe, INEC, ta soke zaɓen.

Shugaban jam’iyyar na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan lokacin taron manema labarai wanda ya gudana a ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar da ke cikin birnin a ranar Larabar.

Abdullahi Abbas wanda mai bai wa jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Barr. Abdul Adamu Fagge ya wakilta, ya ce zaɓen da aka gudanar a ranar Aasabar, 18 ga watan Maris akwai kura-kurai a cikinsa, sannan jami’in tattara sakamakon zaɓe bai bi ƙa’idojin da ya kamata ba Wajen bayyana sakamakon zaɓen.

“akwai mazaɓun da aka samu hatsaniya da kuma inda aka samu sanya ƙuri’u fiye da kima a akwatuna, a irin wannan yanayin da ƙuri’un da aka ce an yi nasara da su ba su kai waɗanda aka soke ba, don haka bai kamata a bayyana wanda ya lashe zaɓen ba, kamata ya yi zaɓen ya zama wanda bai kammala ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, irin abun da ya faru a Kano shi ne ya faru a jihohin Adamawa da Kebbi, kuma a can an bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, amma kuma aka bayyana sakamakon zaɓen na Kano wanda hakan ya saɓa wa dokar zaɓe.

A cewarsa “Sakamakon faruwar abin da aka yi mana, yanzu haka mun tattara lauyoyinmu domin su yi nazari a kan wannan sakamakon da ya bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen, daga nan kuma za mu tafi kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *