APC ta ci zaɓen gwamna a Kuros Ribas

Daga WAKILINMU

Sakamakon zaɓen da Hukumar Zaɓe INEC ta bayyana a ranar Litinin, ya nuna Jam’iyyar APC ce tablashe zaɓen gwamna a Jihar Kuros Riba.

Sanata Bassey Otu shi ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 258,619, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na PDP, Sanata Sandy Onor wanda ya tsira da ƙuri’u 179,636.