APC ta ci zaɓen gwamna a Neja

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin Jam’iyyar APC a jihar Neja, Mohammed Umar-Bago, shi ne ya lashe zaɓen da ya guda a jihar Asabar da ta gabata.

Bago, wanda ɗan Majalisar Wakilai mai ci ne mai wakiltar mazaɓar Chanchaga, ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 469,896, in ji INEC.

Baturen zaɓen, Clement Alawa, ya ce an tabbatar da Bago a matsayin wanda ya ci zaɓen ne bayan cika duka sharuɗɗan da suka dace.

Alhaji Isah Liman Kantigi na Jam’iyyar PDP shi ne ya rufa wa Bago baya da ƙuri’u 387,476, in ji Mr Alawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *