APC ta dakatar da Hon Aminu Sani Jaji kan yi wa jam’iyya zagon ƙasa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a mazaɓar Birnin Magaji dake ƙaramar hukumar Birnin Magaji, jihar Zamfara, ta dakatar da Hon. Aminu Sani Jaji daga jam’iyyar a kan yi wa jam’iyyar zagon ƙasa yayin zaɓen 2023 a jihar.

Aminu Sani Jaji shi ne ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Birnin Magaji da Ƙaura Namoda na tarayya.

Dakatarwa na ƙunshe ne a wata wasiƙa da aka gabatar ga shugaban jam’iyyar APC na jiha mai ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin Magaji, Alh. Bello Lawali Maizogale da Salmanu Umar Tsamiya, inda ake zargin Hon. Sani Jaji da haɗa kai da jam’iyyar adawa ta PDP tare da shirya yadda aka tilasta wa dubban magoya bayan jam’iyyar APC su zaɓi jam’iyyar adawa a mazaɓu huɗu da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji da suka haɗa da, Gora, Kiyawa, Nasarawa Godel Gabas da Damfami/Sabon birni.

A cewarsu, an kafa kwamitin tuntuɓa na mutane takwas da kwamitin bincike na mutum bakwai domin binciken zargin da ake yi wa Hon. Aminu Sani Jaji.

Sun kuma bayyana cewa an aike da takardar gayyata tare da kwafin zarge-zargen a ranar 15 ga watan Yuni 2023 zuwa ga Hon. Aminu Sani Jaji ana buƙatar ya gurfana a gaban kwamitin da kuma amsa tambayoyi zarge-zargen da ake yi masa.

Jam’iyyar ta koka da cewa duk da irin wannan gayyata da kwafin zargin da aka aike masa, ya ƙi bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na mazaɓarsa ta Birnin Magaji tun lokacin.

Sun ƙalubalanci Hon. Jaji kan ƙulla ƙawance a siyasance a baya-bayan nan da Gwamnatin PDP a Jihar Zamfara.

Hakazalika, sun jaddada cewa abinda ya aikata laifuka ne da suka saɓa wa tanadin sashe na 21 (2) na Kundin Tsarin Mulkin APC na 2022 wanda aka yi wa kwaskwarima.