APC ta fitar da sabon jadawalin zaɓen fidda gwani

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC ta fitar da sabon jadawalin zaɓenta na fidda gwani na dukkan matakai.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa hannun Sakataren Jam’iyya na Ƙasa, Felix Morka, a Abuja.

Sanarwar ta nuna Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa (NWC) ya fitar da sabon jadawalin da APC za ta yi amfani da shi wajen gudanar da zaɓen fidda gwani a ɗaukacin matakai.

Kwamitin ya cimma wannan matsaya ne a ranar Litinin, 23 ga Mayun 2022 inda ya nuna yadda zaɓuɓɓukan fidda gawanayen za su gudana kamar haka:

Na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi zai gudana ne a ranar Alhamis, 26 ga Mayu, 2022. Daliget a matakin jiha za su kaɗa wa ‘yan takarar gwamna ƙuri’a, sannan daliget a matakin ƙananan hukumomi su kaɗa wa ‘yan takarar majalisun jihohi ƙuri’a.

Na ‘yan takarar sanata zai gudana ne ranar Juma’a, 27 ga Mayu, 2022, inda daliget a ƙananan hukumomi za su kaɗa ƙuri’a.

Sai kuma zaɓen ‘yan takarar Majalisar Wakilai da za a gudanar a ranar Asabar, 28 ga Mayu, 2022, su ma daliget na ƙananan hukumomi ne za su kaɗa musu ƙuri’a.

Daga nan, sanarwar ta ce zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar Shugaban Ƙasa zai gudana kamar yadda aka tsara, wato Lahadi, 29 zuwa Litinin, 30 ga Mayu, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *