Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jam’iyyar APC a Katsina ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi da ya gudana a jihar.
Shugaban hukumar zaɓen mai zaman kanta a jihar Katsina Malam Lawal Faskari ya sanar wa manema labarai haka a ofishin sa.
Ya ce sai da har yanzu ana jiran sakamakon zaɓe na wasu ƙananan hukumomi.
Lawal Faskari ya bayyana cewa ƙananan hukumomin da ‘yan takarar shugabannin APC suka lashe zaɓe haka kansilolin APC suma nan suka lashe zaɓe.
Sai shugaban hukumar zaɓen bai yi wani ƙarin bayani da ya danganci sauran jam’iyun da suka shige zaɓen da adadin da ita ƙuri’ar da kowace jam’iyya ta samu.
Jam’iyun siyasa biyar ne suka shiga zaɓen,sai dai babban jam’iyar adawa ta PDP bata shiga zaɓen ba.