Daga BASHIR ISAH
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Hon. Diket Pland na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Sanatan Filato ta Tsakiya.
Sa’ilin da yake bayyana sakamakon zaɓen a Pankshin, Baturen zaɓen, Dr. Jima Lar, ya ce Hon Plang ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 131,129.
Yayin da Yohanna Gotom na Jam’iyyar PDP ya rufa masa baya da ƙuri’u 127,022, sannan Garba Pwul na Jam’iyyar Labour ya zo na uku da ƙuri’u 36,510.