APC ta musanta saka sunan Wike a kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamnan Bayelsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da jerin sunayen yaqin neman zaɓen da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Imo, Kogi, da Bayelsa.

A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X (wanda aka fi sani da Tiwita) a ranar Talata, Muhammad Argungu, sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, ya ce Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya amince da kundin tsarin mulkin kwamitin yaqin neman zave tare da tuntuvar Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC).

A cikin jerin sunayen da aka soke yanzu, Dapo Abiodun, gwamnan Ogun, shi ne zai jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Kogi na APC.

Yayin da Inuwa Yahaya, Gwamnan Gombe, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin yaƙin neman zaven jam’iyyar a Bayelsa, sai aka naɗa Bassey Otu, Gwamnan Kuros Riba, a matsayin mai kula da Imo.

Kwamitin yaqin neman zaɓen Kogi, Bayelsa, da Imo na da mambobi 135, 123, da 138 bi da bi.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Mohammed Bago, da Uba Sani sun kasance mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Kogi.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da George Akume, sakataren gwamnatin tarayya (SGF); da Betta Edu, ministar harkokin jinƙai, aka nafa su mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Bayelsa.

Na Imo, Francis Nwifuru, gwamnan Ebonyi; Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai; da Rochas Okorocha, tsohon Sanata; an kuma yi nufin zama mambobin kwamitin yaƙin neman zaven jihar.

Sai dai ‘yan sa’o’i kaɗan bayan fitar da jerin sunayen, jam’iyyar mai mulki a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na qasa Felix Morka ya fitar ta ce jerin sunayen da aka fitar ba wata takarda ce ta jam’iyyar ba.

“An jawo hankalin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan jerin sunayen ‘yan majalisar yaƙin neman zaɓe na ƙasa na zaɓen gwamnonin da za a gudanar a ranar 11 ga Nuwamba, 2023 a jihohin Bayelsa, Kogi, da Imo da ke yawo a sassan kafafen yaɗa labarai. Jerin sunayen ba takardun hukuma ba ne na jam’iyyar don haka a yi watsi da su,” inji shi.

Kafin jam’iyyar APC ta janye jerin sunayen, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT), ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Bayelsa.

Jam’iyyar ta fitar da sunansa a cikin jerin sunayen da aka yi wa kwaskwarima kuma a ƙarshe ta janye komai.