APC ta naɗa Gwamna Lalong daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da nadin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a matsayin darakta-janar na yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na Bola Tinubu. Rahoton Leadership Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. 

Adamu ya samu rakiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da gwamnan jihar Filato, Lalong. 

Shugaban ya kuma bayyana naɗin Ƙaramin Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka Festus Keyamo a matsayin kakakin riƙon ƙwarya kuma mawallafiyar jaridar LEADERSHIP Hannatu Musawa a matsayin mataimakiyar mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *