APC ta naɗa manyan lauyoyin da za su kare nasarar Tinubu a kotu

Daga WAKILINMU

Jam’iyyar APC ta haɗa kan wasu manyan lauyoyi su 12 don su wakilce ta a kotu kan ƙarar da aka shigar kotu dangane da zaɓen Shugaban Ƙasar da ya gabata.

Sanarwar da APC ta fitar ta hannun mai ba ta shawara kan sha’anin shari’a, Ahmad El-Marzuq, ta ce tawagar na ƙunshe da ƙwararrun lauyoyi da suka goge a fagen shari’a zaɓe.

El-Marzuq ya ce lauyoyin za su gudanar da aikinsu ne ƙarƙashin jagorancin fitaccen lauyan nan masanin makamar aiki, wato Prince Lateef Fagbemi.

Ya yi kira ga mambobin APC da su bai wa lauyoyin haɗin kan da ya dace domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito jerin sunayen lauyoyin da tawagar ta ƙunsa kamar haka:

  1. Lateef Fagbemi
  2. Ahmad El-Marzuq
  3. Sam Ologunorisa
    4.Rotimi Oguneso
  4. 5.Olabisi Syebo
    6.Gbotega Oyewole
    7.Muritala Abdulrasheed
    8.Aliyu Saiki
    9.Tajudeen Oladoja
    10.Pius Akubo
    11.Oluseye Opasanya
    12.Suraju Saida
    13.Kazeem Adeniyi

’Yan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyun PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi ne suka shigar da ƙara kotu inda suke ƙalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu a zaɓen a ya gabata.

Sakamakon zaɓen kamar yadda INEC ta bayyana, ya nuna Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726, Atiku ya samu 6,984,520, yayin da Peter Obi ya tsira da ƙuri’u 6,101,533.