APC ta nesanta kanta da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nesanta jam’iyyar da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya kamar yadda shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai suka sanar a ranar Talata.

Yayin taro da Kwamitin Gudanawar na Ƙasa na jam’iyyar da ƙungiyar gwamnonin APC a Abuja, Adamu ya ce Majalisar Tarayya ta saɓa ƙa’ida wajen sanar da manyan jami’an da aka naɗa ba tare da sanin jam’iyyar ba kamar yadda tashar AIT ta rawaito.

A zaman da majalisun suka yi a ranar Talata aka jiyo Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, suka sanar da naɗe-naɗe na manyan muƙamai a majalisar tarayya.

A Majalisar Dattawa, Akpabio ya ambaci Opeyemi Bamidele a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, David Umahi a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye; Mohammed Ali Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye, sai Lola Ashiru a matsayin Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu rinjaye.

Yayin da a Majalisar Wakilai kuwa, Abbas ya ambaci Julius Ihonvbere daga Edo a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, dai kuma Abdullahi Ibrahim Halims daga Kogi a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye.

Kazalika, Abbas ya ambaci Bello Usman Kumo daga Gombe a matsayin Babban Mai Tsawatarwa da Adewunmi Oriyomi Onanuga daga Ogun a matsayin Mataimakin Babban Mai Tsawatarwa.