APC ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

A cikin shirye-shiryenta na tinkarar zaɓen gwamnoni mai zuwa, Jam’iyyar APC mai mulki a Kebbi ta rushe kwamitocin rumfunan zaɓe a jihar.

Alhaji Isah Aslafi jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar ya bayyana wa jaridar Blueprint Manhaja da cewa wannan ya biyo bayan ganin abinda ya faru ne a zaɓen da ya gabata na Shugaban Ƙasa da ‘yan majalisun tarayya wanda ‘mun lura da yadda zaɓen ya bar mu da mamaki, saboda muna ganin muna da nasara amma sai akasin haka ta faru.”

Ya ƙara da cewa duk da yake dai sun yaba da ƙoƙarin da wakilan Jam’iyyar APC suka yi amma dai akwai gyare-gyare a wurare da dama don tinkarar zaɓen gwamnoni.

Wani daga cikin ‘yan kwamitin wata mazaɓa da ke garin Argungu da abin ya shafa da ya so a sakaya sunansa, ya ce, “maganar gaskiya wannan guguwa ce ta taso sanadiyyar tava wax’ɗansu jiga-jigan siyasar Jihar Kebbi da suka haɗa Sanata Muhammadu Adamu Aliero da Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi kuma ba wanda ke da ƙarfin tinkararta saboda maganar gaskiya ba a mori komai ba a mulkin APC a jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Sanata Atiku Bagudu da zai iya alfahari da shi idan aka yi la’akari da irin ayyuka da kuma taimaka wa al’umma da suke yi ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *