APC ta saka ranar da za ta tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta sakar ranar 23 ga Mayu a matsayin ranar da za ta tantance masu sha’awar taka yin takara a jam’iyyar a babban zaɓen 2023 mai ƙaratowa.

Sakataren Tsare-tsare na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Suleiman Arugungun shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, jim kaɗan bayan rantsar da shuwagabanni da sakatarorin kwamitin tantance ‘yan majalisun tarayya, sanatoci da kuma na ‘yan takarar gwamna.

Kamfanin Dillacin Labarai na Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa Jam’iyyar APC za ta yi zaven fidda gwani na Shugaban Ƙasa a ranar 30 ga Mayu zuwa 1 ga Yuni.

“A tantance ‘yan takarar dai a yanzu haka kamar yadda aka sani muna da masu sha’awar yin takarar Shugaban Ƙasa guda 28, wasu daga cikin ‘yan takarar sun fara janye aniyarsu.

“In Allah ya so ya yarda, ranar Litinin 23 ga Mayu, waɗanda suka rage a tantance sosai, za a tantancesu,” inji Arugungun.

NAN ya kuma ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abubakar Kyari shi ne wanda ya rantsar da shugabanni da sakatarorin kwamitin, a madadin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *