APC ta tsayar da ranakun zaɓen fidda gwani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana ranakun 30 da 31 ga Mayu ranakun da za ta yi zaɓen fidda wanda zai cira tutar jam’iyyar a zaɓen Shugaban Ƙasa da ke tafe a 2023.

Sakataren jam’iyyar, Iyiola Omisore, ne ya saka hannu a takardar wanda jam’iyyar ta aika wa hukumar zaɓe.

Idan ba a manta ba hukumar zaɓe ta umarci jam’iyyun ƙasar nan su tabbata sun yi zaɓen fidda gwani da kuma aika wa da sunayen yan takarar kujerun su a farkon watan Yuni.

APC ta ce za ta gudanar da zaɓen kujeran gwamna a jihohi da na majalisar jihohi a ranakun 23 da 11 ga Mayu.

Wato na gwamna ranar 23, na ‘yan majalisar jiha kuma ranar 11 ga Mayu. Za a yi zaɓen fidda gwani na kujerun majalisar tarayya da na dattawa ranar 18 ga Mayu.

Jam’iyyar za ta gudanar da babban taron ta a ranar Laraba mai zuwa wanda shine taro na farko da za ta yi a ƙarƙashin sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ta wanda aka yi a watan Maris.

Idan ba a yi samu jituwa tsakanin ‘yan takaran jam’iyyar musamman kujerar shugaban ƙasa ba, to ko za a yi kare jini, biri jini a wajen zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasar.

Babban dalilin haka kuwa shine ganin jigajigan jam’iyyar da dama sun fito takarar kujerar shugaban ƙasa.

Waɗanda za a fafata a tsakanin su kuwa sun haɗa da Bola Tinubu, Rotimi Amaechi, Rochas Okorocha, David Umahi, Orji Uzor Kalu, Yahaya Bello, da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo da dai sauran su.