APC ta tsinci kanta cikin ruɗani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Har izuwa yanzu Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja bai tabbatar da karɓar ragamar shugabancin jam’iyyar APC na riƙon ƙwarya da tsare-tsare na musamman (CECPC) ba duk da cewa ya jagoranci wani taro a sakatariyar ƙasa a safiyar Litinin.

Bello wanda ya zanta da manema labarai jim kaɗan bayan ya jagoranci taron APC a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin, ya ba da amsoshin tambayoyi masu ruɗani.

Ya ce, “a taron, shugabannin jihohin sun yi rantsuwa a yau, kuma mun tattauna ci gaban da aka samu kan yarjejeniyar da kuma abin da ya kamata a yi nan gaba domin mu cimma ranar 26 ga Maris.

Lokacin da aka tambaye shi a matsayin wa ya jagoranci taron? Ya amsa da “shugaban riƙon ƙwarya? Na jima ina riqo tun lokacin da shugaban ya yi tafiya.

Da aka tambaye shi, “ko za ka iya tabbatar da labarin an naɗa shi a matsayin shugaban riƙo da zai karɓi ragamar mulki daga Buni?

Ya ce, “ka ce labari. Ba sharhi ba.”

Da aka tambaye shi game da matsayin shugaban CECPC a yayin da ake fuskantar tsauraran matakan tsaro a ranar Litinin, gwamnan ya ce, “to, a duk lokacin da aka yi wani babban taro, muna ƙarfafa tsaro.

“A yau mun gudanar da wani babban taro kuma dukkan shugabannin sun shigo domin tabbatar da doka da oda.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin mambobin kwamitin da suka haɗa da Sakatare, Sanata John Akpanudoedrhe, wakiliyar mata, Misis Stella Okotete, shugaban matasa, Mista Ismail Ahmed da kuma Mista David Lyon.

A baya majiyoyi sun yi iƙirarin cewa, an tsige Buni a matsayin shugaban riqo na jam’iyyar APC.

Sai dai da safiyar ranar an yi ta yaɗa wasu faifan bidiyo da ke nuna Sani Bello a Sakatariyar APC ta ƙasa.

A halin da ake ciki, Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa CECPC, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ƙaryata rahotannin cewa an samu sauyin shugabanci a jam’iyyar.

Akpanudoedehe ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce, “an ja hankalinmu kan rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka ɗauki nauyin yi kan canjin shugabanci na gaskiya da aka samu a jam’iyyar APC na riƙon ƙwarya da tsare-tsare na musamman (CECPC).

Sani Bello a matsayin shugaban riqo na APC:

Muƙaddashin shugaban jam’iyyar APC mai riƙon ƙwarya na kwamitin tsare-tsare na babban taron CECPC kuma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya karɓi rahoton kwamitin shiyya na jam’iyyar.

Wannan bayanin a hukumance na Sani Bello a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare na babban taron jam’iyyar APC na CECPC yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar yaɗa labaran gwamnan jihar Neja, Mary Noel-Berje ta sanya wa hannu a ranar Litinin, a haƙiƙanin mai kula da harkokin jam’iyyar.

A cewar Noel-Berje, rahoton da muƙaddashin shugaban jam’iyyar APC, Sani Bello ya samu, shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ne ya miƙa shi a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja.

A cikin wani faifan bidiyo ma gwamnan ya ce, shi ne muƙaddashin shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC.

Da yake karɓar rahoton, CPS ta ce, muƙaddashin shugaban ya yaba wa mambobin kwamitin kan aikin da suka yi.

Tun da farko, shugaban kwamitin jam’iyyar APC na shiyyar kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq wanda ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta samu na yin aiki, ya ce, an kammala aikin kwamitin ne a cikin wa’adin da aka ɗora masa.

Ya kuma yaba wa mambobin kwamitin bisa jajircewarsu wajen samun nasarar aikin.

An ƙaddamar da kwamitin ne domin tabbatar da adalci da daidaiton tsarin raba muƙaman shugabanci a dukkan shiyyoyin siyasar ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *