APC ta yi ra’ayin Akpabio da Barau su jaigoranci Majalisar Ƙasa

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na Jam’iyyar APC (NWC) ya sannar da bin tsarin karɓa-karɓa dangane da shugabancin Majalisar Taraya zubi na 10.

A cewar sanarwar da jam’iyyar ta fitar a ranar Litinin ta bakin Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Felix Morka, tsarin karɓa-karɓar da jami’yyar ta shirya yin amfani da shi ya ƙunshi: Shugaban Majalisar Dattawa – Kudu maso Kudu – Sanata Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa – Arewa maso Yamma – Sanata Barau Jubrin (Kano).

Sauran su ne; Shugaban Majalisar Wakilai, Arewa maso Yamma – Hon. Abass Tajudeen (Kaduna), Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Deputy Kudu maso Gabas – Hon. Ben Kalu (Abia).

Morka ya ce an yanke shawarar kasafta tsarin shugabancin majalisar ne a wajen taron da NWC ya gudanar ranar Litinin bayan tuntuɓa da kuma ganawa da Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce jam’iyyar ta yi kira ga shugabanninta da ma ‘yan Nijeriya da su ci gaba da aiki don cigaban ƙasa a kowane lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *