APC, zaɓe ko naɗi?

Ban ce jam’iyya mai mulki APC na da tasirin mamaye duka faɗin ƙasarmu ba.

Amma dai ga alamu har yanzu ta na da tasiri wajen samun magoya baya idan ta je zaɓe. Zaɓen ranar 11/11/2023 wanda aka gudanar a jihohin Bayelsa, Kogi, Imo tun kafin aje ranar ban hango ma APC rasa jihohin duka ba musamman yadda sau da dama ta ke ƙoƙari wajen nemo ‘yan takara fitattu masu jama’a ta tsayar wanda ta hakan ta ke shammatar jam’iyyun adawa aje zaɓe su zamo yan kallo.

Mu kula da kyau, har kullum ita siyasa abu ce mai buƙatar zurfafa tunani tare da duba inda a ka fito da inda a ka dosa.

Ban ce jam’iyyar APC ta yi kwace ko naɗi ba domin a jihohin Kogi da Imo duk na ta ne don haka ni ke fatan dukkanin zaɓaɓɓun gwamnonin su ba maraɗa kunya wajen aiwatar da shugabanci na adalci da tausayi ga talakawan su.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina.
07066434519/ 08080140820.