APC za ta gana da zaɓaɓɓun ‘yan majalisunta kan shugabancin Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC za ta gana da zaɓaɓɓun sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai ya zuwa ranar Litinin mai zuwa domin tattauna batun shugabancin Majalisa karo na 10 da ake shirin kafawa.

Kwamitin Gudanarwa na jam’iyyar ns Ƙasa ne zai gana da ‘yan majalisun inda ake sa ran samar da tsare-tsaren da za su taimaka wa ‘yan jam’iyyar samun muƙamai a shugabancin majalisun.

Sanarwar taron wadda aka fitar ranar Juma’a da daddare, mai taken “Gayyata zuwa ga ɗaukacin zaɓaɓɓun sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai”, Sakataren jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Iyiola Omisore ne ya rattaba mata hannu.

“Ana sanar da duka zaɓaɓɓun sanatoci da mambobin Majalisar Wakilai na APC zuwa wajen taro tare da shugabancin jam’iyyar na ƙasa.

“Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa za su halarci taron wanda zai gudana Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja,” in ji sanarwar.