Arase ya gargaɗi ‘yan sanda kan cusa kai cikin lamuran filaye da karɓar bashi

Daga SANI AHMAD GIWA

Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda, PSC, Solomon Arase, ya gargaɗi jami’an ‘yan sanda kan zurfafa bincike kan al’amuran filaye, karɓar basussuka da kuma batutuwan da ya kamata a bi ta hanyar warware taƙaddama.

Arase, wanda tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan ne ya yi wannan gargaɗin a lokacin da ya karvi baƙuncin shugabannin kwamitin hulɗa da ‘yan sanda na ƙasa a Abuja.

Jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

A cewar sanarwar, Arase ya yi alƙawarin ci gaba da kasancewa mai fafutukar tabbatar da haɗin gwiwa tsakanin al’umma wajen aikin ‘yan sanda, yana mai cewa ya damu matuqa kan yadda ake samun ƙaruwar cin zarafin bil’adama ga ‘yan sanda.

Arase ya kuma yi alƙawarin yin aiki tare da Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya IGP Usman Baba, domin qara ƙarfafa rundunar ‘yan sandan Nijeriya domin samun kyakkyawan aiki.

A cewarsa, idan ‘yan sanda za su yi fice a harkokinsu na yau da kullum, dole ne a samu sakamako na rashin ɗa’a da kuma fa’ida ga kyawawan halaye, yana mai cewa dole ne a tafi tare.

Ya kuma yi alƙawarin yin ƙoƙari wajen ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin ‘yan sanda na ganin cewa ayyukansu sun yi daidai da ƙa’idojin aiki tare da yin alƙawarin tallafa wa kwamitin a wuraren da suke buƙatar goyon bayansa.

Shugaban kwamitin na ƙasa, Mogaji Olaniya, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bisa naɗin da ya yi masa, inda ya jaddada cewa Arase ya kasance mafi kyawu a wannan aiki.

Mista Olaniya ya ce kwamitin ya je ofishin PSC ne domin taya shugaban murnar naɗin da aka yi masa tare da sanar da shi cewa kwamitin na ci gaba da ginawa kan abubuwan da ya kafa a matsayin IGP na 18.

Ya yi kuma batun qarin girma na musamman ga jami’an ‘yan sanda da suka cancanta don ƙarfafa musu gwiwa wajen ƙara himma a aikin.