‘Arewa Media Writers’ ta gargaɗi matasa kan yaɗa labaran ƙarya

Daga HARUNA UMAR a Jos

Reshen ƙungiyar ‘Arewa media writers’ na jihar Filato da ke fafutukar kawo sauyi a harkar rubuce-rubuce ta kafofin sada zumunta, ta gabatar da babban taron ta na ƙarshen shekarar 2021 don ƙara wa juna sani a kan muhimmancin sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa ta hanyar yaɗa labarai da gudanar da kasuwanci ta yanar gizo.

Taron da ya samu wakilcin manyan marubuta, ’yan jaridu, ƙungiyoyin addini, na siyasa da na cigaban al’umma daga ciki da wajen garin Jos, ya gudana ne  a ɗakin taro na ‘Abba na Shehu Unity Hall’ da ke Babban Birnin Jihar Filato.

A lokacin da ya ke gabatar da jawabin shi, shugaban ƙungiyar reshen Jihar Filato, Malam Abba Abubakar Yakubu, ya ce, ƙoƙarin inganta zaman lafiya da cike giɓin da ke tsakanin mabambantan ƙungiyoyin addini da al’adu a yankin Arewacin ƙasar nan na ɗaya daga cikin manufofin ƙungiyar, yayin da ya ƙara da cewa, ƙungiyar ta na ƙoƙarin samar da haɗin kan matasan Arewa da fahimtar da su haƙƙoƙin da ke kansu na tunatar da shugabanni alƙawuran da ke kansu da matsalolin da talakawa ke fuskanta a ƙasa ta hanyar amfani da hikimomi a rubuce-rubucen su.

Malam Abba ya kuma shawarci matasa da kada su yarda iyayen gidansu ’yan siyasa su yi amfani da su wajen kawo rabuwar kai, rashin zaman lafiya, da cin mutuncin manya, wanda hakan na iya zama musu babbar matsala.

Yayin da ya ke roƙon mahalarta taron da su isar da saƙonnin da suka ɗauka a wajen taron ga waɗanda basu samu zuwa ba, shugaban ya yi alƙawarin aiki hannu da hannu da sauran ƙungiyoyi wajen kawo cigaba a cikin alumma a Jihar Filato da ma ƙasa baki ɗaya.

A lokacin da yake jawabin maraba da baƙi, shugaban taron, Makaman Jos, Injiniya Mansur Salihu Nakande, ya shawarci ƙungiyar da ta ƙara jajircewa wajen fito da matsalolin da suke addabar yankin Arewa ta hanyar amfani da shafukan sada zumunta, tare da saita alƙiblar gwamnati kan ƙalubalen da talakawa a yankin Arewa ke fuskanta, cikin hikimomin rubutu da ka iya janyo hankalin waɗanda abin ya shafa don su kawo ɗauki.

Makaman na Jos ya kuma ƙara jaddada muhimmancin amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa wajen gudanar da kasuwanci da sauran harkokin yau da kullum, kamar yadda a cewar sa duniya ke sauyawa zuwa amfani da na’urar sadarwa a kusan ko ina a masana’antu da hukumomin gwamnati, domin tafiya da zamani.

A lokacin da yake gabatar da muƙala a kan alaƙar da ke tsakanin kafafen sadarwa na zamani da labaran ƙarya, Dr Murtala Sani Hashim, malami a Kwalejin koyar da aikin jarida ta NTA da ke Jos, ya koka a kan yadda wasu daga cikin masu amfani da kafafen sadarwa na zamani ke yaɗa ƙirƙirarrun labarai da ake kire da ‘fake news’ a Turance.

Ya ƙara da jan hankalin marubuta da su guji rubutu ko yaɗa duk wani nau’in magana, hoto, ko sauti da ka iya kawo tashin hankali a cikin al’umma.

Mista Kabir Ishaq, masanin fasahar sadarwa, Malam Ahmad Suleiman mai nazari kan harkokin kasuwanci, da kuma Hajiya Kaltume Auwal malama a Jami’ar Jos na daga cikin waɗanda suka yi jawabi a taron, inda suka ƙara jaddada muhimmancin amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen tallata hajoji da sanin me duniya ke ciki, suna masu yin kira ga al’umma da su yi watsi da duk wani labari da ba su da cikakkiyar masaniya a kai.