Arewa ta Tsakiya na kwaɗayin shugabancin APC na ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Yankin Arewa ta tsakiya ya nuna ƙudirinsa na neman shugabancin jam’iyyar APC a matakin ƙasa.

Yankin ya bayyana sha’awarsa kan neman shugabancin jam’iyyar ne sa’ilin da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar a yankin suka ziyarci Gwamnan Neja kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, Abubakar Sani Bello, s fadar gwamnatin jihar da Minna, babban birnin jihar.

Yayin da yake bayani kan irin gwagwarmayar da yankin ya sha dangane da yi wa APC hidima tun bayan kafiwarta, Gwamna Sani ya ce bai kamata a baro yankin a baya ba.

Yana mai cewa sun amince su shiga a fafata da su duk kuwa da cewa sauran shiyyoyi su ma sun nuna kwaɗayinsu game da neman shugabancin jam’iyyar.

Gwamnatin Jihar Neja ta wallafa duka waɗannan bayanan a shafinta na twita jim kaɗan bayan kammala taronsu a ranar Talata.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*