Armenia ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci

Armenia ta sanar da amincewa da Falasɗinu da a matsayin ƙasa wadda ke zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta yi hakan, tana mai cewa tana adawa da cin zarafin fararen hula.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkoin wajen ƙasar ta fitar, ta ce a ƙudurinta na tabbatar da dokokin ƙasa da ƙasa da daidaito tsakanin ƙasashe da wanzar da ‘yancin kai da zaman lafiya da juna, hakan ne ya ba ta kwarin gwiwar amincewa da Ƙasar Falasdinu.

Ƙasar wacce ita kanta ta ke fama da rikici da makwabciyarta Azarbaijan shekaru da dama, ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke gudanar da ayyukan soji a Gaza, tana mai cewa tana da matuƙar sha’awar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsawon lokaci a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ƙasashe da dama sun amince da Ƙasar Falasdinu ana tsaka da yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas, inda suka sha kakkausar suka daga jami’an Isra’ilan.