Arsenal ta lallasa Everton karo na 100 a tarihi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Arsenal ta ci Everton 4-0 a kwatan wasan Firimiya da suka kara ranar Laraba a Emirates.

Wasa ne da ya kamata su fafata tun ranar 11 ga watan Satumbar 2022.

Arsenal ta ci qwallo ta hannun Bukayo Saka saura minti biyar su yi hutu, sannan Gabriel Martinelli ya ƙara na biyu daf da cikar minti na 45.

Kyaftin ɗin Arsenal, Martin Odegaard shine ya ƙara na biyu, saura minti 19 a tashi daga karawar daga baya Martinelli ya aara na biyu na huɗu a wasan.

Wannan shine karo na 100 da Arsenal ta ci Everton a babbar gasar tamaula ta Ingila a wasa 204 da canjars 43, Everton ta yi nasara a 61.

Sun kara ranar 4 ga watan Fabrairu a Goodison Park, inda Everton ta ci 1-0 ta hannun James Tarkowski a minti na 60 a gasar ta Premier.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a matakin farko a kan teburin Premier da maki 60, bayan karawa 25 a Premier ta bana.

Karon farko da Gunners ta haɗa maki 60, bayan wasa 25 a Premier, wadda ta taba yin wannan kwazon a kakar 2003-04 da kuma a 2007-08.

Ta kuma bai wa Manchester City tazarar maki biyar, wadda take ta biyu mai riƙe da kofin bara.

Everton ta ci gaba da zama a mataki na 18 cikin ‘yan ukun ƙarshe a teburin bana da maki 21.