Asalin ƙabilar Babur

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙabilar Babur tana danganta asalinta ne da Mutanen Yamen, don haka aka ruwaito cewa rundunar wasu mutane ne suka ƴi hijira daga ƙasar Yemen a wajajen shekara ta 600 miladiyya suka riski Ƙasar Sudan, sannan suka shigo cikin Sahara tare da sauka a yankin da Ƙabilar Babur ke rayuwa a yanzu cikin ƙasar Borno.

Ba iya ƙabilar Babur ba, har ƙabilun Kanuri da Luguda da wasunsu da ke rayuwa a wannan yankin suna iƙirarin asalin kakanninsu daga Yemen suke. Gusawar zamani ne kurum ya sanya takamaimen tarihinsu ya sauya. Zuwa yanzu dai, ana samun ƙabilar Babur ne a Jihohin Borno da Adamawa.

A jihar Borno, akwai ƙabilar Babur a garuruwan Biu, Hawul, Kwaya kusar, Shani, Kwajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa, Wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yimirshika, Hyera, Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam, Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdang, Bula tawewe, Kogu Tashan Alade, Kida, da hang shang da kuma Bayo, amma a jihar Adamawa ƙabilar Babur sun fi yawa a garin Garkida cikin ƙaramar hukumar Gombi. Dukkan waɗannan garuruwa da ƙabilar Babur ke zaune ciki na da nasu tarihin.

Misali, an ce jarumin da ya kafa daular mulki ta biyu mai suna Yamta, ɗa ne ga wata mace ’yar ƙabilar Mandara. Wai Tun tana da cikinsa aka ɗauke ta zuwa gidan Sarkin Borno, don haka a can aka haifeshi kuma a can ya taso da tarbiyar Kanuri.

Amma da Yamta ya girma, sai ya tumbatsa wajen jarumta. Shi ne fa har ya karɓe ikon yankin da Biu ta ke a yau tare da kafa masarauta.

Ana ganin ya fara kafa mazaunin masarautarsa ne a wani wuri mai suna ‘Limbur’ tsakanin chikorkur da Mandagarau. Har zuwa yanzu kuma an ce kabarinsa yana nan a Limbur ɗin.

Ƙabilar Babur, su ne ke da rinjaye a garin Biu da wasu garuruwan makwabta, amma akwai kuma ƙabilar Bura wadda ke zaune a maƙwabciyar ƙasar Babur ɗin, mai suna ‘Babur Bura’. Dukkansu kusan da yare ɗaya suke amfani, kuma yaren yana da kamanceceniya da na garuruwan Chibok, Marghi, Higgi, Kilba and Bazza.

An fi samun ƙabilar ‘Babur Bura’ a jihohin gabashin Nijeriya, watau Borno, Adamawa, Gombe da Yobe.

Al’adun aure:
Mafi yawan ƙabilun Borno musamman Kanuri, Shuwa Arab da Babur na da kamanceceniya wajen al’adun auratayya. Wataƙila hakan ya faru ne saboda jimawar ƙabilun wajen zaman tare ko kuma ana iya cewa kakanninsu ne ɗaya, don haka daga gare su suka yi gadon ɗabi’un.

Bisa al’ada ta Ƙabilar Babur, idan namiji ya ga mace yana so, to ba zai sanar ma ta ba, sai dai ya nemeta da abota.

A wannan abotar ne zai rinƙa bincikar halayyarta dana magabatanta, ba tare da ta sani ba, daga bisani kuma sai ya samu wani dattijo a danginsa ya ɗora masa alhakin kammala masa bincike akan yarinyar da zuriyarta duka.

Daga wannan matakin kuma sai mai neman auren ya zaɓi maza uku da mata biyu aƙalla, daga danginsa su raka shi gidan su yarinyar.

A nan ne za su haɗu da iyayenta ko ’yan uwanta, har kuma a tambayeta abinda ke tsakaninsu da wannan mai neman auren na ta, da kuma muradinta akansa da sauransu. Idan an aminta a ƙulla auratayya, to daga nan ne za a sanya ranar yin baye, suna kiranta ‘Yuyma’.

Idan ranar ta zo, dangi za su haɗu daga ɓangaren namiji da mace maza da mata a gabatar da kayan ci dana sha, sanna a sanya ranar aure, watau ‘Mbwa Nyika’.

Dangane da batun kuɗin aure ko sadaki, namiji na iya bayar da dukkan abinda ya samu gare shi ga iyayen wadda yake so ya aura, sukuma za su ciri wani abu kaɗan su mayar masa da ragowar, (wasu ma an ce basa cirar kome), to amma za a gabatar masa da sunayen wasu abubuwa da ake so ya saya ma ta.

A hakan ma, ba dole bane ya sayi dukkan komai ba, kawai dai yana iya zavar abinda ya ke da iko ne ya saya. Idan namiji ya haɗa kayan, sai ya tashi ’yan uwansa su ta fi suka yi gidan su yarinya. Daga nan kuma za a saurarar ranar ɗaura aure.

Ɗaura aure kuwa ya danganta da addinin da mutum yake bi, kasancewar addini ya yi tasiri cikin ƙabilar Babur, don haka Kiristocin cikinsu sukan je coci ne domin ɗaura aure, yayin da Musulman cikinsu kan ɗaura aure a Masallatai ko gidaje, tare da aiwatar da al’adun aure kalar wanda Musulunci ya halatta.

Tasirin al’adun auratayya da lafiyarsu:
1.     Kasancewar Ƙabilar Babur tana da sauƙi gami da rangwame wajen qulla auratayya, hakan na ragewa mazajen cikinsu tashin hankalin fita neman abin duniya ta ko wanne hali domin samun ɗiyar aure.

2.     Hakan kuwa na iya zamowa abu mafi dacewa da ke sasanta tunanin mazajen gami da raguwar aikata kananun laifuka da kuma ingantuwar lafiyar kwakwalwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *