Asalin ƙabilar Ibo a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamar sauran ƙabilun Nijeriya, tarihin al’umar Ibo shi ma yana tattare da bayanai da zato da fahimta da ra’ayoyi iri daban-daban, har ma da jayayya a tsakanin masana tarihi, musamman ma game da asalin inda al’ummar ta Ibo ta samo tushenta, inda masana tarihi da dama suke ikirari cewa, al’ummar ta Ibo ta samo asalinta ne daga Isra’ila, don haka tana da dangantaka da Yahudawa.

Kuma daga can ne Ibon suka fito, har suka iso wajen da suka samu mazauni na dindindin a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Harshen Igbo wani vangare ne na dangin harsunan Nijar-Congo. Kuma ya kasu kashi zuwa yaruka da yawa na yanki kuma ana iya fahimtar juna tare da babbar ƙungiyar ‘Igboid’. Ƙasar Ibo ta ratsa qananan Kogin Neja, gabas da kudu na ƙungiyoyin Edoid da Idomoid, da yamma na ƙungiyar Ibibioid (Cross River).

Kafin zamanin Turawan mulkin mallaka na Biritaniya a karni na 20, ƙabilar Ibo ƙungiyar siyasa ce da ta wargaje, tare da wasu manyan sarakuna kamar Nri, Aro Confederacy, Agbor da Onitsha. Frederick Lugard ya gabatar da tsarin Eze na ‘shugabanni masu bada umarni’. Ba tare da yaqin Fulani ba da yaɗuwar addinin Musulunci a Nijeriya a cikin ƙarni na 19, suka zama Kirista da yawa a ƙarƙashin mulkin mallaka. Dangane da mamayar mulkin mallaka, Ibo sun sami ƙarfi na nuna bambancin ƙabila. A lokacin yaƙin basasar Nijeriya na 1967-1970, yankunan Ibo suka ɓalle a matsayin Jamhuriyar Biafra wacce ba ta daɗe ba. Ƙungiyar ‘Movement for Actualization of the Sovereign State of Biafra’, ƙungiyar da aka kafa a shekarar 1999, na ci gaba da gwagwarmaya ba tashin hankali don neman ƙasar Ibo mai cin gashin kanta.

Sarautar Ibo:
Masana irin su Ibenekwu (2017) da kuma Osabiya (2017), sun siffanta salon mulkin Ibo kafin zuwan Turawa da salon mulkin tarayya da kuma dimokuraɗiyya wanda yake cike da daidaito; daidaito da ma’ana ta rarraba damar shugabanci ga duk wanda ya cancanta ba tare da la’akari da fifikon damar da wani yake da ita a kan wani ba.

Kafin zuwan Turawa yankin Ibo ba su da wata tabbatacciyyar hanyar gudanar da mulki ko kuma wata dawamammiyar doka ta dindindin. Haka nan kuma babu wata masarauta mai tushen sarautar da ake gado ƙwaya ɗaya rak!

Matakin shugabancin Ibo yana farawa ne daga ƙaramin mataki zuwa babba ba tare da samun shugaba guda ɗaya rak ba a sama. Tushen shugabancin yakan fara ne daga haula; tattaruwar ɗaiɗaikun gidaje da ke da dangantaka ta jini a tsakaninsu, wacce ka iya zama a nesa ko a kusa. Sannan kuma babbar kujerar shugabancin Ibo ita ce gari; wanda yake samuwa daga haɗuwar unguwanni da kuma ƙauyuka.

Dukkan wani hukunci da za a ɗauka wanda ya shafi al’ummar Ibo, to akwai Oha-na-eze wacce ke da ma’ana ta majalisar dattawa da ke da alhakin gudanar da mulki da jagorancin al’ummar da abin ya shafa ta ke wuyanta. Wannan majalisa ta dattawa ba majalisa ce ta dindindin ba, ta kan zauna ne a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Sannan kuma, wakilcin ɗaiɗaikun garuruwa ne ya ke samar da ita. Haka nan shugabancin zaman yakan iya faɗawa a kan kowa ta hanyar la’akari da shekaru. Wato kenan idan tsoho mafi shekaru a cikin wakilai ya shugabanci zama, to sai kuma yam utu kafin wani zaman, to za a sake duba wanda ya fi shekaru ya jagoranci zaman.

Kafin kaiwa ga waccar majalisa ta dattawa, akwai matakan shugabanci a ƙasar Ibo guda huɗu kamar haka:

  1. Iyali, makatin farko na shugabancin Inyamurai shi ne matakin Iyali, wanda namiji babba yakan zama jagora a gida. Wato mai gida. Dukkan ragamar jagorancin gida da suka haɗa da kare mutunci, rarraba ayyuka, sasanto tsakanin masu rigima da sauransu, ya ɗoru a wuyan mai gida.
  2. Haula, gidaje ne masu yawa amma kuma dukka suna da dangataka ta jini. Uba ko Okpara; wato kaka, mafi yawan shekaru na ɗaya daga cikin gidajen da cikin wannan haular shi ya ke zama jagora.
  3. Ƙauye, gari ne ƙarami, wanda hauloli da yawa suke samarwa, a mafiya yawan lokuta akan taras da cewa kusan dukkan irin waɗannan ƙauyuka ana samu sun haɗu da junansu ta fannin dangataka a nesa ko a kusa. Namiji mafi yawan shekaru a haular da ta fi kowace haula daɗewa a wannan ƙauye shi yakan zama shugaba.
  4. Gari, shi kuma ƙauyuka ne suke bunƙasa su zama gari, wanda kuma shi ne mataki mafi girma na sarauta a ƙasar Ibo kafin zuwan Turawa.
  5. Majalisar Dattawa.
    Duk da wannan salon shugabanci na Ibo wanda ba a gadonsa, suna kuma da muƙamai na girmamawa a siyasance, waɗanda ake baiwa mutane. Ƙari akan haka kuma, akwai wasu yankuna da kuma manyan biranen kasuwancin Inyamurai da ke kewayen Kogin Neja, kamar irin su Anaca, Awka, Oguta da kuma tsohuwar masarautar Nri, waɗanda tun kafi zuwa Turawa sun fara gudanar da salon mulki irin na sarautar da ake gada.

Saboda haka, akwai muƙamai irin su Eze, Igwe, Obi da sauransu a ƙasar Inyamurai, waɗanda wasu na sarauta ne, wasu kuma na girmamawa. Muƙami mafi daraja a matakin sarautar Inyamurai, ba gadonsa ake yi ba. Duk wanda ya cancanta yakan ɗare wannan kujera ta hanyar zaɗe ba tare da la’akari da shekaru, kuɗi ko kuma dangin da ya fito ba.

Mulki:
Ƙasar Ibo tana da tsarin gudanar da mulki kamar haka:

  1. Mulkin Ƙauye: Shi dai qauye, ɗaiɗaikun haloli ne suke samar da shi. Kowace haula guda ɗaya da ke ƙauye tana da shugaba guda ɗaya da ake kira Ofo, tattaruwar waɗannan Ofo-Ofo na ƙauye guda su ke samar da majalisar dattawa wacce ita kuma ita take da alhakin gudanar da mulkin ƙauyen.
  2. Sa’ance (Sa’a): Sa’ance a nan na nufin abokan haihuwa. Sa’anace abu ne mai matuƙar muhimmancin a tsarin gudanar da mulki a ƙasar Ibo. Ayyuka da suka haɗa da samar da tsaro; gyaran gari da ya shafi sharer hanya, gina hanya, sharar kasuwa, sare itatuwan kan hanya, da sauransu; aiwatar da doka-da-oda da majalisar dattawa suka samar; tabbatar bin doka-da-oda; gudanar da bukukuwan al’ada; da sauran abubuwa masu tarin yawa.

Saboda haka a dunƙule, kusan dukkan wani abu da za a yi a al’ummar Ibo, akwai sa’annin juna da ya kamata a ɗorawa wannan nauyi. Ita kanta majalisar dattawa shekaru ne kai mutum. Haka nan akan samu mutane masu wasu adadin shekaru ya zama su ke gadin gari, haka shara, gudanar da bukukuwan al’ada da sauransu. Sukan yi amfani da tazarar shekaru biyu tsakanin wannan sa’ance da wanca. Kenan, duk wanda aka haifa a tsakanin shekaru biyu sun zama sa’annin juna. Amma idan mutum ya grime da shekaru biyu, to ya zama na gaba da kai.

Bayan haka kuma, akwai muƙamai irin su Ozo, Ama da Ekpe da ake baiwa duk wani mutum wanda yake bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawo cigaba a ƙasar Ibo.

Haƙiƙa, duk wanda aka baiwa wannan muƙami ya zama abin girmamawa a cikin al’ummar Inyamurai, a wasu lokutan idan shekarunsu sun kai akan basu dama ta jagorantar zaman majalisar dattawa.

Shari’a:
A al’adar Ibo, kowane yanki na al’umma, yana da iya shari’ar da zai iya aiwatarwa. A matakin farko, mai gida shi ke da alhakin ɗaukar dukkan matakin da ya dace idan aka samu savani a gida. Wanda ka iya zama sasanto ko kuma aiwatar da hukunci.

Sa’ance, dukkan wasu jama’a masu shekaru kusan ɗaya, su na da cikakkiyar damar hukunta ƙananan laifuffukan da suke aiwatar a tsakaninsu.

Laifuffuka da suka ƙetare iyakokin gidaje, haula da kuma sa’ance, to sai a gurfanar da su a gaban majalisar dattawa don ɗaukar matakin da ya dace. Manya-manyan laifuffuka kamar irin su kisan kai, laifin zina, da sauran makamantansu, su kuma suna danganta abin ne da allolinsu. Akwai Ala, a matsayin babban sarkin da Ibo suka yi Imani da shi. Ana kuma kaiwa gare shi ne ta hanyar wasu.

Bayan dukkan waɗannan, shekaru, suna da matuqar tasiri a cikin al’ummar Ibo. Suna matuƙar girmama na gaba da su, wanda kuma wannan abu shi ma tun daga gida ya ke farawa. Haihuwar farko a gida, shi ne wanda kowa dole ya girmama shi a gida. Ɗan farko namiji suna kiran sa da Opara, mace kuma Ada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *