Asalin Fulani da shigarsu Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ci gaba da kawo muku tarihin manyan qabilun Nijeriya, yau ma Jaridar Manhaja za ta yi duba kan ƙabilar Fulani, wadda ɗaya ce daga cikin manyan ƙabilu mafi yawan jama’a a Nijeriya.

Tushen Fulani:
Fulani dai ƙabila ce da tarihi ke turke asalinta tun ƙarni na 15 daga wasu manyan ’yankuna biyu da ke ƙasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jalloh.

Daga nan ne suka ci gaba da bazuwa cikin ƙasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa. Ko da yake babu tsayayyen adadi na yawan Fulani a duniya, amma kiyasi na nuna yawansu ya kai aƙalla miliyan 45, kuma sun fi yawa ne a ƙasashen yammacin nahiyar Afirka. Masanna tarihin Fulani sun ce, baya ga yammacin Afirka, Fulani na nan a ƙasashe da dama na nahiyar musamman tsakiyarta.

Suka ƙara da cewa, Fulani sun fi yawa a Nijeriya sannan suna da yawa a ƙasashen:

  • Guinea Conakry
  • Guinea Bissau
  • Mali
  • Senegal
  • Gambia
  • Mauritania
  • Kamaru
  • Niger
  • Sudan
  • Saliyo
  • Burkina Faso da kuma
  • Chadi.

Shigarsu Ƙasar Hausa:
Wasu masu tarihi sun nuna wata ƙungiya ta Fulani sun fito daga ƙasar Sham wato ɗaya daga cikin ƙasashen Larabawa har suka zo Futatoro suka shigo ƙasarnan a rarrabe.

Wani sashe na masu tarihi suna ƙarfafa cewa, Fulani ƙabila ɗaya ce, kuma daga tushe ɗaya suke. Sun shigo ƙasar Afirika ta yamma wato ta qetaren ƙasashen Larabawa daga wajen ƙasar Masar daidai gavar kogin Nilu, sai suka bazu a manyan ƙasashen Afirika irin su Libiya da Laberiya da Maroko da Aljeriya da Mali da Barkina-Faso har suka ƙwararo cikin Nijeriya ta Arewa. A wata faɗar kuma an ce, Fulani sun fito daga ƙasar Sanagal.

Fulani da suka shigo ƙasar Hausa jinsi ɗaya ne, sai dai sun kasu kashi biyu. Akwai Fulanin gida, waɗanda ake wa laqabi da Fulanin soro sannan akwai masu yawon kiwo a daji masu zaga ƙasa-ƙasa gari-gari ana yi musu laƙabi da Fulanin Daji (Makiyaya).

Ƙasashen Fulani:
Wata ɗabi’a da aka san Fulani da ita ce yawo da dabbobi daga wata ƙasa zuwa wata, kuma wannan ne dalilin da ya sa ake samun su a ƙasashe da dama musamman a nahiyar Afirka.

Jihadin Ɗan Fodio da masarautun Fulani a Nijeriya:
Jihadin Shehu Usmanu Bin Fodio ne babban dalilin bazuwar Fulani a Nijeriya, inda shehun ya kafa dauloli da kuma masarautun Fulani a arewacin ƙasar, a cewar Dakta Abubakar Girei, malami a sashen nazarin harshen Fulfulde a kwalejin ilimi ta tarayya da ke Yola.

“Jihadin Shehu Ɗan Fodio ne ya kafa kusan manyan masarautun da ke arewacin Nijeriya inda ya danqa wa malamai kuma shehunai jagorancin waɗannan yankuna saboda adalcinsu, ba sarakuna ba kamar yadda ake cewa yanzu. Wannan shi ya sa Fulani suka fi yawa daga cikin waɗanda ke riqe da masarautun,” a cewar Dakta Girei.

Manyan masarautun Fulani a Nijeriya sun haɗa da:

  • Masarautar Fombinah ta Modibbo Adama
  • Masarautar Sokoto
  • Masarautar Kano
  • Masarautar Zazzau
  • Gwandu
  • Katsina
  • Gombe da sarauransu.

Masarautar Modibbo Adama:
Masarautar Modibbo Adama tana ɗaya daga cikin manyan masarautun Fulani a duniya wacce Shehu Usmanu Bin Fodio ya miƙa wa tuta, kuma tarihi ya nuna an kafa ta ne shekara 212 da suka gabata, wato tun shekarar 1808.

Modibbo Adama shi ne sarkin Masarautar Fombinah wato Lamido Fombinah na farko kuma masarautar da ke da fada a Yola ta ratsa yankuna da yawa daga Nijeriya har ƙasar Kamaru.

Zuwa yanzu dai ta samar da sarakuna 12 daga kan Modibbo Adama zuwa Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha.

A gidan adana kayan tarihin masarautar Modibbo Adama da ke Yola, akwai kayan tarihi daban-daban ajiye. Ciki har da farar tuta ta ainihi da Shehu Usman Bin Fodio ya danƙa wa Modibbo Adama yayin kafa masarautar a shekarar 1808.

Sauran kayan tarihin sun haɗa da kore da kayan yaƙi na gargajiya kamar sulke da garkuwa da takubba da dai sauransu.

Fulanin Soro: Galibinsu dogaye ne, wankan tarwaɗa, kuma akan samu farare da baƙaƙe. Sannan masu kyawawan idanuwa ne da dogayen yatsu na ƙafa da na hannu. Yawancinsu makaranta Alƙur’ani da littattafan tauhidi da sauran littattafan koyarwa na addinin Musulunci.

Sana’arsu kiwo na cikin gida da noma. Halayensu kuwa sun haɗa da kunya da haquri da yin liyafa ga baƙi da iya jagorancin jama’a. Fulanin gida ne kuma suka raya mulki na Musulunci a Arewacin Nijeriya.

Fulanin Daji (Makiyaya): Yawancinsu farare ne fat, kuma kyawawan gaske kamar Larabawa. Wasu kuwa wankan tarwaɗa ne, amma akan samu baƙaƙe kaɗan a cikinsu. Suna da yawan gashi, mazansu da matansu. Fulanin daji ne suka fi wauta da jarunta, ga su da ƙarfin hali da dauriya.

Sana’arsu kiwon dabbobi da saka irin ta kaba. Al’adarsu kuwa yawan tashi daga wannan wuri zuwa wancan suna tafe suna ta bushe-bushen sarewa, suna nema wa dabbobinsu abinci. Sukan zagaya ƙasashen da ake samun ciyawa a bakin kogi musamman lokacin rani. Basa son zama a cikin gari sai dole. Sukan shiga gari ne kawai don sayen kayan masarufi.

Ƙarin Harshen Fulani:
Kamar yadda Fulanin ke da masarautu da dama haka ma kuma suke da ƙarin harshe kala-kala wanda masana tarihi suka kasa kashi shida. Wannan ne ma ya sa ba lallai ne wasu Fulanin Nijeriya su fahimci Fulatancin wasu ’yan uwansu da ke qasashe kamar Senegal da Gambiya ko kuma Burkina Faso ba. Ko da a Nijeriya, akwai wani ƙarin harshe da wasu Fulanin ba su fahimtarsa.

Akwai manyan qarin harshe na Fulani guda shida ban da ƙanana da ke cikinsu, na farko akwai.

  • Futa Toro
  • Futa Jallohn
  • Masina
  • Sokoto
  • Adamawa
  • Arewa ta tsakiya

Al’adun Fulani da alaƙarsu da shanu:
An san ƙabilar Fulani da manyan al’adu waɗanda a yau ƙabilu da dama ke kwaikwayo. Babbar al’adar da aka san Bafulatani da ita ita ce kiwon shanu da tumaki da kuma awaki. Wani abun da mutane da dama za su so su sani shi ne alaƙar da ke tsakanin Bafulatani da saniya.

A cewar Dakta Ahmad Shehu masanin tarihin Fulani kuma malami a sashen nazarin harsuna da ke Jami’ar Bayero ta Kano ya ce, alaƙar Bafulatani da saniya alaƙa ce da tafi ko wacce ƙarfi a al’adar Bafulatani.

“‘Nagge woni Pulaaku’, ‘Pulaaku woni Nagge’, ma’ana kasancewar Bafulatani cikakke shi ne ya mallaki saniya,” inji Dakta Ahmad Shehu.

Dakta Saleh Momaleh masanin al’adun Fulani kuma malami a sashen nazarin harkokin noma a Jami’ar Bayero da ke Kano ya ce, wasu manyan al’adun Fulani bayan kiwo sun haɗa da.

  • Siffar Kunya
  • Karatu
  • Girmama mutane
  • Sharo
  • Hawan Daba
  • Auratayya tsakanin ‘yan uwa

Gudunmawar Fulani ga samun ’yancin kan Nijeriya:
Fulani na daga cikin manyan ƙabilun da suka taimaka wajen sama wa ƙasar ’yanci daga Turawan mulkin mallaka. Baya ga zaratan sojoji na Fulani da suka yi gwagwarmaya, akwai kuma fitattu da suka taimaka wajen sama wa Nijeriya ’yanci.

Dakta Abubakar Girei na kwalejin ilimi ta tarayya da ke Yola ya ce, “tun kafun samun ’yancin kai akwai jamhuriyya da ke ƙarƙashin gudanarwar Fulani wacce ake kira ‘Sokoto Caliphate’.

“Wannan jamhuriyyar ta taka muhimmiyar rawa wajen sama wa Nijeriya ’yancin kai saboda akwai mutane kamar Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto wanda Bafulatani ne kuma jika ga Shehu Usman Bin Fodio, ya yi gwagwarmaya sosai wajen sama wa Nijeriya ’yanci.”