Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ghana, Asamoah Gyan ya sanar da yin murabus daga buga ƙwallon ƙafa.
A wata sanarwa, Gyan ya ce lokaci ya yi da zai ajiye aikin taka leda a cikin mutunci.
Ɗan wasan ya ci kwallaye 51 daga wasanni 109 daya buga wa ƙasarsa, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan Ghana a ya fi cin ƙwallaye a tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.
Ɗan wasan mai shekaru 37 ya fara sana’ar ƙwallon ƙafa ce a shekarar 2003 tare da ƙungiyar ƙwallon Liberty Professionals, inda daga bisani ya koma Turai, ya fara yi wa Udinese ta Italiya wasa a gasar Seria A, daga nan ya koma Rennes a Faransa da kuma Sunderland a Ingila inda ya nuna bajinta.
Gyan ya ɗan murza tamola a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tare da ƙungiyar Al Ain, inda ya taimaka mata ta lashe gasar League ɗin ƙasar, bayan da ya ci ƙwallaye 28 daga wasanni 32, abin da ya sa ya zama ɗan wasan da ya fi cin ƙwallaye.
Ya buga wa tawagar ƙwallon ƙafar Ghana wasanni a gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekarar 2006, 2010 da 2014.