Ashe duk ma tsoffin kuɗi ne a bankunan!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk wanda ya shiga bankuna a makon nan har ma a baya-bayan nan zai amince da ni cewa ya ga tsoffin kuɗi a jere inda kuma duk wanda ya nema za a ba shi bayan ya bi layi a kan kantar banki ko dogon layi na ATM. Wasu bankunan ma sai an raba lamba a na kira tamkar waɗanda a ke biya kuɗin ƙwadago bayan gudanar da aikin leburanci ko ma yadda a ke yi a shekarun baya a kwaso kuɗin albashin ma’aikata a buhu a shigo ofishin jami’in biya (CASHIER) a na kiran sunaye ma’aikata na bin layin sunan sa, su na sa hannu su na karɓar ’yan kuɗinsu in ma canji ya rage a yi wa jami’in alheri da shi don in an zo biyan na wani watan a tseguntawa ma’aikaci mai alheri ya riga sauran zuwa karɓa ko kuma ya matsa lamba don karvar hannun kuɗin adashensa.

Kai wani abun dubawa ma shi ne har wata leda a ka yi amfani da ita a ka layyace kuɗin kamar alfowar rufe laya inda sai an yage ledar kafin a iya fito da kuɗin. Haka za ka ga an jawo kuɗin an jera kan keken ƙidaya ka ji warrrrrrrrrrrrrrrr har kura ta tsoffin kuɗi ta tashi sannan sai a lissafa adadin kuɗin da mutum ya buƙata a ba shi. Banki mai haxa zumuntar dole don duk wani tabaron mutunm ko wani ɗaure kunkumi da bel ba zai hana mutum bin layi da saurarawa sauran mutane ba.

Kuma za ka ji a na hira da nuna takaicin wanda ke da laifi tsakanin babban banki, gwamnan bankin Godwin Emefiele ko kuma gwamnatin shugaba Buhari. Mutane da kuɗin su amma ɗaukar kuɗin ya zama babban jidali kamar bin layin mai a gidan mai wanda mutum kuɗin sa zai lale ya biya a zuba ma sa amma in bai yi sa’a ba sai ya kwana a layin gidan mai. Tun mu na muhawara da wasu jami’an banki kan yanayin da Lebanon ke ciki na karayar tattalin arziki da ya sanya bankuna ba sa iya biyan masu ajiya kuɗinsu cewa irin hakan na tinkaro Nijeriya su na cewa a’a har makamancin hakan ya zo ya tabbata.

A yayin da a Lebanon a kan yi zanga-zanga da cinnawa bankuna wuta don samun ’yan kuɗin sayan abinci sai ga shi a kudancin Nijeriya an samu irin wannan akasin. Kawai bambancin Nijeriya a kan samu masu tsawatawa ne a duk yanayin da a ka shiga za a samu wa imma malaman addini, sarakunan gargajiya ko wasu dattawa da in sun yi magana a kan yi haƙuri a saurare su. In ƙasa ta rasa wazanda za su tsawata a daina wani abu ko rai ba ya so to za a iya shiga halin da sai yanda hali ya yi kawai.

A Lebanon fa har wata mata sai ta kai ga ta ɗauki bindigar roba ta faɗa banki ta yi barazanar buɗe wuta kafin ta samu kuɗin ta inda daga bisani a ka gano ai harbin iska ne. Mutane kan shiga banki da makamai a miƙa mu su kuɗinsu don dole a birnin Beirut inda da zarar sun fito sai su mika kuɗin ga ’yan uwan su ko waɗanda su ka aminta da su daga nan sai su miƙa wuya ga ’yan sanda. Duk yadda Naira ta kai ga faɗuwa kan canjin dala to kuɗin Beirut sun faɗi fiye da haka nesa ba kusa ba.

Lebanon fa har sojojin ta na kuka da cewa su na fama da yunwa don haka ƙasashe ke tura agajin abinci da magunguna don taimakawa sojojin. Tsoffin sojojin ƙasar ma sun yi zanga-zanga kwanan nan da ƙorafin an bar su da yunwa don su na zuwa banki amma ba sa samun ’yan kuɗin fanshon su. Duk yadda whalar rayuwa ta zo a Nijeriya a kan samu sauƙi daga bisani. Har yanzu Nijeriya ba ta kama hanyar zama tamkar Lebanon ba amma matsalolin sun yi kama da na Lebanon ɗin.

Bari ma dai in dan ƙara ƙaimin magana don ina ganin Allah ne ya kiyaye don da barazanar nan ta yajin aiki da mamaye ofisoshin babban bankin Nijeriya ya tabbata a Larabar nan da ta gabata, da kuwa an ga hushin ’yan ƙasa na zahiri. Saurin da a ka yi a ka zauna da shugabannin ƙwadagon ƙarƙashin sabon shugaban ta Joe Ajeoro ya taimaka wajen rage kaifin matakin.

An gani a zahiri yadda babban bankin ya sako tsoffin kuɗi tukuf-tukuf don jama’a su samu da na ji mutane na cewa tsoron barazanar ƙungiyar ƙwadago ne don kafin nan ba alamar yin hakan. Wannan ƙungiya mai membobi a ko ina a ƙasar nan da ke kuma fusace don dama albashin bai taka kara ya karya ba, kuma a ka ce su yi yajin aiki don za a ɗau matakan tilasta babban bankin ya samar da kuɗi, ai kuwa da sai yadda hali ya yi.

Duk kukan talakawa da kiraye-kiraye daga kowane ɓangaren jama’a ya faɗa kan kurman kunne don ba wata amsa mai daɗi da a ke samu, amma ka ga da ya ke wata ƙungiya mai lasin ta yi barazana shikenan sai a ka ɗau matakan gaggawa don yayyafa ruwa kan ƙurar da ta kunno kai. Yajin aikin ƙungiyar ƙwadago zai shafi illahirin ƙasar ne ta ƙasa da ta sama da ta teku. Aƙalla dai a Abuja mutane sun ga canji a bankuna ta hanyar samun tsoffin kuɗi ’yan Naira 1000.

In an miƙawa mutum kuɗin da ya buƙata sai ka ga ya ƙidaya su ya tura a aljihun da ɗan sane ba zai samu dama a kan sa cikin sauqi ba. Wai wuya mai koyawa mutane adana. Ko dai Naira ba ta da daraja a canji kan kuɗazen ƙetare amma ta na da daraja adana ta a aljihu don a kan same ta da wuya. Kuma yanzu dai masu ƙananan sana’a’i da masu neman sadaka za su iya samun taimako. Allah ya sa sauƙi ya ɗore a Nijeriya don hakan ya ƙara hana tashin wata fitina da ka iya aukuwa in matsi ya yi yawa.

Ina sabbin kuɗi ne?

Ni na yi tsammanin ganin a na gauraya sabbi da tsoffin kuɗi a bankuna kamar yadda Kotun Ƙoli ta yanke hukunci har zuwa Disamba amma gaskiya tsoffin kawai na gani. Me ke hana buga sabbin kuɗin ne ko kuma yin fenti da kuɗin kamar yadda Emefiele ya faɗa? Ko takardun kuɗin da a kan yi wa fentin sun ƙare ne? amsoshin nan sai masana ba daga gama-garin mu masu duba lamuran daga gefe ba.

Duk da haka a kan ga sabbin kuɗin a hannun ’yan jari hujja amma ba kan kantar banki ba. Ƙalubalen Nijeriya kenan yadda mutane ke zama daba da juna da wagegen bambanci tsakanin talakawa da ’yan jari hujja. Ai a baya kuma mun ji labarin yadda wasu talakawa kan yi koyi da ’yan jari hujja ta inda su ke haɗa kai da wasu a bankuna da ke tsegunta mu su labarin an zuba kuɗi a na’urar ATM don haka sai su garzayo da gudu su zo su ɗiba kafin saura da ba su da mai ba su labari su ankara. In mu na son Nijeriya ta samu cigaba mai ma’ana sai mun riƙa taimakawa juna da kuma kare mutuncin ƙasar ko buƙatun ƙasa a farko gabanin buƙatun kashin kai.

Gaskiya ’yan Nijeriya na son sanin inda buga sabbin kuɗi ya shiga don har dai a ka cigaba da amfani da tsoffin kuɗin har zuwa Disamba to me zai faru kenan? Ko sai an sake komawa kotu a ƙara wa’adin tsoffin kuɗin zuwa kwatar shekara ta 2024? Masana kuɗi da wasu da su ka dan yi tafiye-tafiye ƙasashen duniya sun ba da shawarar a cigaba da amfani da kuɗin har sai sabbin sun rinjayi tsoffin, wato ya zama ba ranar soke amfani da wata takardar kuɗi. Bankuna kan iya janye tsoffin ko tsufa ma ya sa a daina amfani da su.

Tun da ba a yi amfani da irin wannan shawarar ba a Nijeriya kamar yanda wasu manyan ƙasashen duniya ke yi, to akwai wata manufa da a ke son cimmawa! Shin an cimma manufar zuwa yanzu, shin manufar ta shafi babban zaɓen 2023 ne? in haka ne ai zabe ya wuce sai dai ko batun ƙara a kotuna da nan ma kuɗi ke aiki musamman wajen ɗaukar lauyoyi da sauran su. Duk wannan wahalar indai tsoffin kuɗi za a cigaba da bayarwa to talakawa ba za su fahimci dalilan gwamnati na jefa su a cikin wahala ba.

Kammalawa;

Fata a nan yadda shugaba Muhammadu Buhari ya shiga a na ta murna a 2015 ya yi wani abu da za a riqa kewarsa bayan ya sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023. Zuwa yanzu dai ban ji mutane na nuna damuwa cewa shugaba Buhari zai sauka daga mulki ba. A kan damu da rabuwa da gwani don tunanin in ya kau za a samu maida hannun agogo baya ga irin nasarorin ma da ya cimma. Shin daga 2015 zuwa 2023 na mulkin Buhari hannun agogon mulkin Nijeriya gaba ya yi ko baya?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *