Ashe Osinbajo ba ɗan Tinubu ba ne?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Mazauna Legas dai sun san sunan mataimakin shugaban Nijeriya mai ci Yemi Osinbajo gabanin zaven 2015 amma a gaskiya yawancin mutanen Nijeriya sai lokacin da shugaba Buhari ya canko shi ya zama ma sa mataimakin ɗan takara sannan ne sunan sa ya fito a ka san shi. Hakanan wasu musamman ’yan Arewa ba sa iya ambatar sunan sa sosai sai ka ji sun ce OSIBANJO maimakon OSINBAJO.

In ka ɗebe tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, a dimokuraɗiyyar Nijeriya ba wani mataimakin shugaba da ya daɗe kan kujera irin Osinbajo. Gabanin zaman sa mataimakin shugaban Nijeriya, ya riƙe kujerar kwamishinan shari’a ne a Jihar Legas. Ɗan asalin jihar Ogun da tsarin haɗa kan Yarbawa su koma kan dandamalin siyasa ɗaya da Bola Tinubu ya ƙirƙiro ya ba shi damar. Hakanan akwai wasu ma daga sauran jihohin Yarbawan da su ka shiga ko ci gajiyar dogon mafarkin Tinubu na mayar da Yarbawa kan siyasa ɗaya da za ta taka rawa a dunƙule a lamuran tarayya. Tun a lokacin yunƙurin ƙulla ƙawancen jam’iyyu a 2011 don neman kada PDP a ka fahimci irin burin Tinubu.

A wancan lokacin kamar Tinubu na neman haɗa kai da su CPC ta shugaba Buhari don ba mamaki jama’iyyar sa ta AC ba ta gama kama qasa sosai ba. Hakanan ba mamaki Tinubu ya fi hango a 2015 lokacin Jonathan ya ƙara baƙin jini sai ya ƙulla haɗakar don sauƙin karvar gwamnatin tarayya da amfani da ƙuri’u miliyan 12 da Buhari ke samu kyauta daga talakawan arewa. Kazalika an ba da labarin yadda Tinubun ya gana da tsohon shugaba Jonathan a Legas bayan wargajewar shirin ƙulla ƙawancen.

In za a tuna AC ta tsayar da tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci Mallam Nuhu Ribadu a matsayin ɗan takarar shugaba. Abin mamaki yayin da AC ta samu gagarumar nasarar gwamnoni a jihohin Yarbawa amma duk da haka ba ta samawa Ribadu matsayi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa ba. Hakan ya ƙarfafa hasashen AC ba ta damu da tasiri a tarayya ba a lokacin inda kuma ba ta soki lamarin lashe kujerar da PDP ƙarƙashin Goodluck Jonathan ta yi ba.

Ko ma a zaɓen 2015 inda babbar jam’iyyar adawa ɗaya da a ka kafa APC ba ta samawa Buhari ƙuri’un fitar hankali a yankin Yarbawa ba in a ka kwatanta da jihohin arewa irin su Kano, Kaduna, Bauchi, Sokoto da sauran su. Masu sharhi a lokacin sun ce ko PDP ce ta lashe zaɓen ba za ta koka da cewa jihohin Yarbawa sun tsane ta ba. Wannan na nuna raba kafa ta fuskar manufa ko ra’ayin siyasa a kudu maso yammacin Nijeriya.

Yanzu dai abin da ya fito fili ya kuma zama abin sharhi shi ne martanin Bola Tinubu ga fitowa takarar Osinbajo inda duk da yadda alaƙarsu ta zama mai dogon tarihi amma ga burin takarar shugaban ƙasa sun raba layi don Tinubu ya ce Osinbajo ba ɗansa ba ne. Wato ma’ana Tinubu na cewa ba ɗansa da ya kai tasirin zama ko tsayawa takarar shugaban ƙasa. Tinubu na magana ne a taron gwamnonin APC guda 12 da ya yi wa jawabi a gidan gwamnatin Kebbi da ke Abuja.

Tinubu dai ya zauna da gwamnonin don neman su mara ma sa baya a takarar tikitin APC da ya shiga. Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu da ke jagorantar ƙungiyar gwamnonin na APC ya tabbatar da buƙatar da Tinubu ya miƙa don su duba su nazarci muradin. A tsarin siyasa ba a fitowa a kafafen labaru a mara baya ga wani ɓangare gabanin gudanar da zaɓen fidda gwani.

Duk da haka akwai gwamnonin da tuni su ka yi wa Tinubu mubaya’a. Masu sharhi kuma ba su tsaya a nan ba don su na ganin har gobe Tinubu ya na tare da Osinbajo inda duk za su fito takara amma da zarar ɗaya ya samu tikiti sai ɗayan ya mara baya don cigaba da tafiya a Inuwar daular siyasar Yarbawa da Tinubu ya kafa. Ba za su rasa ganin wani lokacin in a na son kushe manyan siyasar arewa sai ka ga an sa hoton Tinubu da manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati waɗanda ya tallafawa har su ka cimma buri.

Cikin na kan gaba da a ke tallen da shi akwai Osinbajo sai a biyo baya da irin su Babatunde Fashola, Sunday Dare, Akinwummi Ambode, Babajide Sanwo Olu, Lai Muhammed, Olarumumbe Mamora, Femi Gbajabiamiala da sauran su. Wannan batun kan su a haɗe ya ke ko bakin su ɗaya hasashe ne na masu sharhin siyasa. Abin da zai bayyana lamarin a fili shi ne yanda za a ga takun gwamnonin Yarbawa.

Matuƙar su ka zauna su haɗe su ka yi mubaya’a ga ɗaya daga ‘yan takarar biyu to magana ta fito fili. Hakanan idan ɗaya ya janye wa ɗaya gabanin zaɓen fidda gwani to nan ma za a gane dawar garin. A gaskiya idan har sai an tafi zaɓen fidda gwani kuma a ka kai ga kaɗa ƙuri’a to nan fa lissafin zai sauya salo ko za a iya cewa ba a gano gaskiyar manufa ko kuma manufar ta samu tangarɗa a lokacin aiwatarwa.

In an duba tsarin APC ga babban zaɓen na 2023 na nuna tura tikitin takarar shugabancin ga yankin kudancin Nijeriya. Akasarin waxanda zuwa yanzu ma a jam’iyyar da su ka nuna aniyar takara daga kudun su ke. An samu manya biyu daga kudu maso yamma ‘yan gida xaya wato Tinubu da Osinbajo sai kuma a kudu maso kudu Rotimi Amaechi daga Ribas ya fito.

A kudu maso gabar kuma ga su nan da yawa kamar Dave Umahi, Rochas Okorocha da Orji Kalu. Bayanan yiwuwar takarar Goodluck Jonathan a APC ba ta tabbata ba duk yawan ganin sa da a ka riqa yi a fadar Aso Rock da hakan ya qarfafa hasashen za a ba shi dama ya yi takara in ya so tun da shekara huxu zai yi bisa tsarin mulki, sai a sake juyo da akalar ga ‘yan siyasar APC na arewa. Mulkin karva-karva dai ba tsarin dimokraxiyya ba ne amma da alamu ‘yan siyasar da muradun darewa kan madafun iko da kare buqatun vangaranci na neman maida hakan tilas.

PDP ta faro tsarin a 2007 amma bai tafi yadda a ka yi muradi ba don rasuwar tsohon shugaba Umaru ‘Yar’adua inda Jonathan da ya kammala wa’adi ya ƙi saduda sai ya yi takara da zarcewa kan karaga inda har ma ya sake gwadawa a 2015 amma bai samu nasara ba.

Sharhi;

Biyo bayan mafi girman mai muƙami baya ga shugaba Buhari a gwamnatin APC Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana niyyar takarar shugabancin Nijeriya a 2023, an shiga duba yanayin tagomashin sa a takarar. Ga shi ya na cikin fadar Aso Rock amma ba lalle ba ne ya na aiki bisa amincewar fadar ko kuma a ce ya na da goyon bayan fadar 100% a wannan muradin na sa. Fitowar sa da gabatar da jawabin neman takarar ta kafafen sadarwa ya kawo ƙarshen layin kira da ƙungiyoyin da ke buƙatar ya fito takarar ke yi har da samun gagarumin ofishin yaɗa wannan manufa a Abuja.

Osinbajo wanda ya shiga jerin akasarin ‘yan kudu wajen neman kujerar, zai shiga takara da maigidan sa Bola Tinubu matuƙar jam’iyyar ba ta fidda ɗan takara ta hanyar daidatawa ba gabanin zaɓen fidda gwani.

Tuni Osinbajo ya shiga amfani da duk wata damar magana wajen ambata gwagwarmayarsa a gwamnati. Osinbajo wanda a yanzu ya shiga ba da misalan ayyukan da ya yi lokacin ya na kwamishina a Legas, ya faɗi hanyoyin da zai bi wajen inganta lamuran ƙasar ciki da tabbatar da hukumomin gwamnati na aiki tare bisa manufa ɗaya, ƙarfafa zuba jari da tara haraji. Osinbajo wanda lauya ne ya faɗi dabarun da ya tava bi wajen tabbatar da saurin gudanar da shari’a da ya ke cewa duk ƙasar da ba ta da tsarin shari’a mai inganci ba za ta kai labarin cigaba ba. Hakanan ya yi magana kan wasu matsoli na yunƙurin azurta kai da karɓar na goro a matsayin hanyoyin da ke nakasa cigaban ƙasashe masu tasowa.

Mai taimakawa shugaban Nijeriya kan siyasa Gambo Manzo wanda ya yi aiki da Osinbajo tun a Legas ya ce zai iya yi wa ‘yan Nijeriya adalci. Manzo ya zayyana Osinbajo da jagoran da ba ya nuna ƙabilanci ko bambancin addini. Hakanan ya ce ya kware a harkar shugabanci tun da ya samu damar riqon mulki har sau uku lokacin da shugaba Buhari ba shi da lafiya. Tuni ƙungiyoyi su ka bayyana don yayata muradin takarar Osinbajo a kudu da arewa. Jagoran magoya bayan na kudu Olawale Shodeinde ya yi kira ga shugaba Buhari da duk masu ruwa da tsaki na APC su marawa Osinbajo baya. Shodeinde bai kawo batun Bola Tinubu ba.

Kammalawa;

Tangarɗar da takarar Osinbajo ke fuskanta ko da ma a ƙaddara zai samu tikiti ita ce furta shin zai ɗora daga inda shugaba Buhari ya tsaya ne ko kuwa a’a? hakanan zai so shugaba Buhari ya daga hannun sa ko zai yi gaban kai kamar yadda Algoe ya yi zamanin tsohon shugaban Amurka Bill Clinton.

Kazalika wasu manyan jama’ar shugaba Buhari na daridari ga Osinbajo don yadda ya kwabe tsohon shugaban hukumar DSS Lawal Daura da a ke hasashen shugaba Buhari na ƙauna da kuma manufofin zuba dala a kasuwa don daga darajar Naira wani lokacin da shugaba Buhari ya ba shi muqaddashi. Waɗanda su ka samu sanyin guiwa ga salon jagorancin shugaba Buhari har cewa su ke yi gara Osinbajo da Buhari ko kuma su ce ai Osinbajo ya fi shugaba Buhari fasahar gudanar da shuganci mai tasiri. Shin kunne zai girma har ya fi kai? Lokaci ne zai nuna don ko ma dai yaya Osinbajo ya yabawa aikin da ya gudanar ko ya ke gudanarwa da shugaba Buhari da zayyana shugaban da wani mutum mai daraja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *