Asibitin Aminu Kano zai fara dashen ɓargo – Mahukunta asibitin

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, AKTH, da ke Kano, a ranar Litinin ya ƙaddamar da wani sabon sashin kula da cututtukan jini kuma hakan ya nuna cewa za a fara dashen ƙargo a cibiyar.

AKTH zai kasance asibitin koyarwa na biyu a Nijeriya da zai riƙa yin dashen ɓargo a ƙasar.

Babban Daraktan Asibitin, Farfesa Abba Sheshe ne ya bayyana haka a wurin ƙaddamar da cibiyar a hukumance, wanda wani Injiniya Umar lbrahim ya bada ita a matsayin gudunmawa.

Ya bayyana cewa asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas ne kaɗai ya yi nasarar dashen ɓargo a Nijeriya.

Ya kuma jaddada cewa kayan aikin da za a sanya a cibiyar za su sanya a samu nasarar dashen ɓargo a asibitin.

Ya yaba wa mai bayarwa lbrahim, kuma ya yi addu’ar Allah ya saka masa da alkhairi.

Da yake jawabi a madadin mai bayar da tallafin, Farfesa Mahmoud Daneji, ya ce an yi hakan ne domin tunawa da marigayiya mahaifiyarsa.

Ya kuma yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar ayyukan da aka gudanar a unguwar, da su yi wa mahaifiyar wanda ya bada gudunmawar addu’a, da shi kansa da kuma dukkan iyalanta.