Aston Villa ta cimma yarjejeniyar ɗaukar Duran

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aston Villa ta cimma yarjejeniyar ɗaukar ɗan ƙwallon tawagar Colombia, Jhon Duran daga Chicago Fire.

Duran, mai shekara 19, ya ci ƙwallo takwas ya kuma bayar da shida aka zura a raga a wasa 28 da ya yi wa Chicago.

Kammala yarjejeniyar ta alakanta idan an auna koshin lafiyar ɗan wasan, sannan idan ya samu takardar shaidar aiki a Burtaniya.

Ɗan ƙwallon zai yi takara a gurbi ɗaya da Ollie Watkins da Danny Ings a ƙungiyar da Unai Emery ke jan ragama, bayan da ‘yan wasan biyu suka ci ƙwallo bakwai a tsakaninsu.

Duran ya buga wa tawagar Colombia wasa uku, kuma duka canjin ɗan ƙwallo ya yi.

Villa tana mataki na 11 a teburin Premier League na kakar nan.