Aston Villa ta shirya sayen ɗan wasan Nijeriya, Ndidi

Ɗan wasan tsakiyar Nijeriya da Leicester City, Wilfred Ndidi, ya ce, ba shi da sha’awar barin Leicester City a yanzu, duk da shirin Ƙungiyar Aston Villa ke yi na miƙa tayin Fam miliyan 50 kan shi.

Jaridar Daily Star ta Burtaniya ta ruwaito cewa, Villa ta kammala shirye-shiryen taya Ndidi, kuma idan har ciniki ya faɗa a ƙarshen kaka zai zama ɗan wasan mafi tsada da ƙungiyar ta tava saye a tarihi.

Ndidi ya buga wa Leicester wasanni 23 a bana, inda ya ci wa Foxes ɗin ƙwallo ɗaya.

To, sai dai tsohon ɗan wasan Genk din ya ce, “ina jin daɗin wasa da rayuwa a Leicester. Iyalina suna nan, ga shi ina karatun digiri kan kasuwanci.”

A bara Aston Villa ta sayi Emiliano Buendia daga Norwich City a kan fam miliyan 34, saboda haka idan ƙungiyar ta iya sayen Ndidi kan fam miliyan 50 zai zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin ƙungiyar.

To, amma mai horar da Leicester Brendan Rodgers ya ce, ɗan wasan nasa ya haura abinda Villa ke son biya kansa.

Yanzu haka Ndidi na da sauran yarjejeniya da Leicester daga nan zuwa 2024.

Leicester City na fuskantar koma baya a bana, inda suka kasa cin wasa ko ɗaya a cikin biyar, kuma suna zaune a na 11 a teburin Firimiyar Ingila.

Ta kuma ƙare na biyar kakar wasanni biyu da suka wuce.

A jiya da daddare ne Wilfred Ndidi ya yi wa Leicester wasa na 200 a kofin Europa Conference League da za su buga da Randers FC a filin King Power.