Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Ƙasa (ASUP) ta janye yajin aikin gargaɗi na makonni biyu da ta yi, inda ta buƙaci ɗaukacin malaman da su koma ranar 30 ga Mayu, 2022.
Hakan ya fito ne daga bakin sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa, Abdullahi Yalwa.
A cewarsa, ƙungiyar na buƙatar mambobin ƙungiyar da su dawo bakin aiki daga ranar 30 ga watan Mayu, 2022, tare da fatan gwamnati za ta yi amfani da damar da aka ba ta don magance abubuwa biyar da ake neman a wajenta.
A ranar 16 ga Mayu, 2022, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na tsawon makonni biyu kan gazawar gwamnati wajen biyan wasu buƙatu.
Wasu daga cikin buƙatun da ƙungiyar ta zayyana sun haɗa da biyan Naira biliyan 15 a asusu na farfaɗo da masana’antar ƙere-ƙere; biyan mafi ƙarancin albashi; sake duba yanayin ayyuka, da sauransu.
Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan yajin aikin, ta fara biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata ga malaman jami’o’in da sauran ma’aikatan manyan makarantun ƙasar nan.