ASUU ta ƙara mako takwas a kan yajin aikin da take yi

Daga SANI AHMAD GIWA

Yayin da a yau Litinin wa’adin yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) take yi, ƙungiyar ta kuma sanar da tsawaita yajin aikin da makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan buƙatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka ƙulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a a ƙasar.

Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau, jami’i ne a ƙungiyar ta ASUU, ya ce sun ɗauki matakin ƙara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun ƙara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.

Ya ce makonni 8 sun wadatar matuƙar gwamnatin da gaske take kan ɗaukar matakin da ya dace.

ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanya ta ƙarshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Nijeriya biya mata buƙatunta.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne ƙungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), ta tsunduma yajin aikin gargaɗi ga gwamanatin Nijeriya na tsawon wata guda.

Wasu bayanai sun nuna cewa ƙungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Nijeriya mulkin dimukuraɗiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *