ASUU ta ƙi amincewa Tinubu ya bai wa jami’o’i cin gashin kansu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU) ta yi watsi da shirin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na bai wa jami’o’in cikakken ’yancin cin gashin kai, tana mai cewa ba zai yiwu gwamnati ta tsame hannunta daga bayar da tallafin karatu ga manyan jami’o’i ba.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 15 ga Satumba, 2023, yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television na Sunrise Daily.

Ya na mayar da martani ne kan wani rahoto da Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa gwamnati za ta ɓullo da sabbin hanyoyin bayar da tallafin karatu ga manyan makarantu ta hanyar bai wa jami’o’i cikakken ’yancin cin gashin kai don gano sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.

Osodeke ya ce, Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya bayyana ƙarara cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta ɗauki nauyin karatun jami’o’in gwamnati.

“Babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce ba za ta tallafa wa jami’o’in gwamnati ba, domin a can ne a doka. Akwai a Kundin Tsarin Mulki, duba sashe na 18 na Kundin Tsarin Mulki, ya ce ‘Jami’a, Firamare da Sakandare ’yanci ne,” in ji Osodeke.

Yayin da Osodeke ya amince cewa gwamnati na iya neman sabbin hanyoyin da za ta tallafa wa jami’o’i, ya ce, ba za ta iya janye tallafin gabaɗaya ba. Ya ƙara da cewa, idan gwamnati ta kyale jami’o’in su riƙa gudanar da ayyukansu bisa ƙa’ida, bisa tanadin doka, za su iya samun isassun kuɗaɗe don gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *