ASUU ta soma yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta soma yajin aiki don neman cimma buƙatunta a wajen Gwamnatin Tarayya.

ASUU ta bayyana soma yajin aikin nata ne ga manema labarai a wannan Litinin.

Da yake yi wa manema labarai bayani kan matakin da suka ɗauka bayan kammala tattaunawar yini biyu da shugabbanin ƙungiyar suka yi, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yajin aikin nasu na tsawon wata guda ne a matsayin gargaɗi ga gwamnatin ƙasa.

Ya ce tun a ranar Asabar da ta gabata shugabannin ASUU na ƙasa suka soma zaman tattaunawa a Jami’ar Legas kan batun.

Ya ƙara da cewa kafin soma zaman nasu, sai da suka sanar da malamai da ɗalibai na jami’oin faɗin ƙasar nan game da dalilin da ya sa ASUU za ta tsunduma cikin yajin aiki.

Malaman sun ɗauki matakin shiga yajin aiki ne saboda rashin gaskiyar da suka ce gwamnatin tarayya ta nuna musu na ƙin cika musu yarjejeniyar da suka cimma a baya, yarjejeniyar da ta yi sanadiyyar janye yajin aikin da suka yi a 2020.

Farfesa Osodeke ya ce duk da tattaunar da suka yi da Ministan Ƙwadago, Dr. Chris Ngige a Oktoban 2021, kan batutuwan da suka haɗa da farfaɗo da jami’o’in gwamnati, biyan kuɗaɗen alawus, biyan kuɗaɗen ƙarin girma, batun tsarin biyan albashi na IPPIS da sauransu, babu ko guda da aka aiwatar daga jerin buƙatun nasu.

A baya-bayan nan, an ji Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bada tabbacin gwamnatinsa za ta daraja duka yarjejeniyoyin da aka cimma da ASUU don hana aukuwar yawa-yawan shiga yajin aikin a fannin ilimin ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *