ASUU ta tsawaita yajin aikinta da mako huɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i a Nijeriya ta ASUU ta bayyana matakin tsawaita yajin aikin da take yi da mako huɗu.

Dama ASUU ta shafe sama da watanni biyar tana yajin aikin bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin Nijeriya, yanzu kuma ga shi ta ƙara wata ɗaya.

Idan har aka shafe wasu makonni huɗu ba a sasanta tsakanin gwamnati da ASUU ba, hakan na nufin ɗaliban jami’o’in sun shafe rabin shekara suna zaman jiran tsammani a gida.

Sanarwar da ASUU ta fitar na ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke, an kuma fitar da ita ne bayan kammala wani zaman gaggawa na jiga-jigan ƙungiyar ranar Lahadi a Abuja.

Haka ma ASUU ta gode wa ƙungiyar Ƙwadago ta NLC, da sauran ƙungiyoyin da suka mara mata baya wurin yin zanga-zangar nuna goyon baya da nufin kawo ƙarshen yajin aikin.

Ƙungiyar Malaman Jami’ar ta ƙara da cewa ta tsawaita yajin aikin ne da mako huɗu, lura da cewa har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta nuna wata alama ta kawo ƙarshen zaman ɗaliban a gida ba.

Tun a ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, bisa zargin gwamnatin Nijeriya da gaza cika alƙawuran da ta ɗauka a yarjejeniyar da suka ƙulla, ciki har da batun inganta rayuwar malaman da kuma dambarwar shigar da ƙungiyar tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnatin ta fito da shi.